logo

HAUSA

An dakatar da ‘yar Nijeriya a wasannin Olympics na Tokyo saboda amfani da kayan kara kuzari

2021-07-31 16:26:27 CMG

An dakatar da ‘yar Nijeriya a wasannin Olympics na Tokyo saboda amfani da kayan kara kuzari_fororder_0731-Okagbare-Faeza

An dakatar da ‘yar wasan tsere ta Nijeriya Blessing Okagbare, daga wasannin tseren mata a matakin kusa da na karshe a wasannin Olympics na Tokyo, bayan gwaji ya nuna ta yi amfani da kayan kara kuzari.

Sashen yaki da amfani da kayan kara kuzari a tsakanin ‘yan wasan guje-guje da tsalle-tsalle AIU, ya ce ya dakatar da Blessing na wucin gadi bayan samfurinta da aka dauka ya nuna akwai sinadarin kara kuzari a jikinta.

A cewar sashen na AIU, ya karbi samfurin ne a ranar 19 ba a lokacin wasa ba, inda wani dakin gwaji da hukumar WADA mai yaki da amfani da kwayoyi a tsakanin ‘yan wasa ta duniya, ta amince da shi, ya sanar da sakamako a jiya Juma’a.

Bisa dokokin hana shan kayakin kara kuzari, Blessing Okagbare na da damar neman a sake gwajin samfurin domin tabbatar da sakamakon. (Fa’iza Mustapha)

Faeza