logo

HAUSA

Adadin lambobin Zinare da Sin ta samu a wasannin Olympics na Tokyo, ya dara wanda ta samu a wasannin Olympics na Rio

2021-08-03 14:14:59 CRI

Adadin lambobin Zinare da Sin ta samu a wasannin Olympics na Tokyo, ya dara wanda ta samu a wasannin Olympics na Rio_fororder_QQ图片20210803140426

Kasar Sin ta lashe lambobin Zinare 5 a wasannin da suka hada da na daga karfi da keke da harbi da wasan kasada, yayin wasannin Olympics na Tokyo da aka yi jiya Litinin, wanda kuma shi ne adadin Zinare mafi yawa da ta samu cikin kwana guda a wasannin dake gudana.

Yayin da ya rage kwanaki 6 a rufe gasar, yawan lambobin Zinare da Sin ta samu ya kai 29, adadin da ya haura da guda 3 kan wadanda ta samu a wasannin da aka yi a Rio a 2016. Har ila yau Sin na da lambobin Azurfa 17 da Tagulla 16 daga wasannin na Tokyo dake gudana.

Amurka ce a matsayi na biyu a yawan lambobin Zinare, inda take da 22, da sauran lambobi 64, sai Japan mai masaukin baki da take matsayi na 3 da zinare 17 da azurfa 6, sai kuma tagulla 10. (Fa’iza Mustapha)