logo

HAUSA

Yankin Guangdong-Hong Kong-Macao Greater Bay zai samar wa matasan Hong Kong dandali mai kyau

2021-03-11 14:01:04 CRI

Yankin Guangdong-Hong Kong-Macao Greater Bay zai samar wa matasan Hong Kong dandali mai kyau_fororder_src=http___5b0988e595225.cdn.sohucs.com_images_20181206_051ff53d820246feb7f25bfca6c9a832.jpeg&refer=http___5b0988e595225.cdn.sohucs

An tanadi tsari na “wajibcin tabbatar da samun dawamammen yanayi na kwanciyar hankali da wadata, a yankunan musamman na Hong Kong da Macao, tare da saukakawa matasan Hong Kong da Macao damar yin karatu, da samun aikin yi, da habaka cinikayya” cikin daftarin shirin shekaru biyar-biyar na bunkasa tattalin arziki da zamantakewar kasar Sin na 14.

Wasu ‘yan majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta kasar Sin, wadanda suka fito daga Hong Kong da Macao suna ganin cewa, yankin Guangdong-Hong Kong-Macao Greater Bay mai yawan zarafi, zai kasance kamar wani dandali ne ga matasan Hong Kong, na samun damar cimma burinsu.

A cikin shekaru 2 da ake aiwatar da kundin shirin raya yankin Guangdong-Hong Kong-Macao Greater Bay, an fara amfani da layin dogo mai saurin tafiya na Guangzhou-Hong Kong, da kuma babbar gadar Hong Kong-Zhuhai-Macao daya bayan daya, kana ana gudanar da aikin gina cibiyar kimiyya da fasaha da yin kirkire-kirkire ba tare da wata matsala ba.

Kaza lika ana kyautata yanayin kirkire-kirkire da habaka sana’a, ta yadda ake kara bukatar kwararru masu yawa. A farkon wannan shekara, Hong Kong ta gabatar da shirin samar da guraben aikin yi a yankin Guangdong-Hong Kong-Macao Greater Bay, don bai wa daliban Hong Kong da suka gama karatu daga shekarar 2019 zuwa 2021 guraben aikin yi dubu 2, ciki had da wasu 700 dake aiki a fannin kimiyya da kirkire-kirkire.

Ban da haka kuma, Hong Kong ta fitar da wasu shirye-shirye, na karfafa gwiwar matasan Hong Kong, ta yadda za su iya habaka sana’a a yankin na Guangdong-Hong Kong-Macao Greater Bay. (Tasallah Yuan)

Tasallah Yuan