logo

HAUSA

Sin na matukar adawa da dakatar da lasisin kafar CGTN dake watsa shirye shirye a Birtaniya

2021-02-05 20:38:15 CRI

Kakakin ma’aiktar harkokin wajen kasar Sin Wang Wenbin, ya ce Sin na matukar adawa da matakin da hukuma mai lura da kafofin watsa labarai ta Birtaniya ta dauka, na dakatar da lasisin kafar watsa shirye-shirye ta CGTN ta kasar Sin reshen kasar Birtaniya.

Wang ya ce matakin hukumar, na da nasaba da siyasa da banbancin akida, tare da siyasantar da wasu batutuwa, matakin da ya yi matukar gurgunta matsayin kasar Sin, ya kuma illata matsayin cudanyar kasashen biyu, wanda yanayi ne da kasar Sin ba za ta lamunta ba.

Tuni dai rahotanni suka tabbatar da cewa, hukumar dake lura da kafofin watsa labarai ta Birtaniya, ta dakatar da lasisin kafar CGTN, mai watsa shirye shirye a Birtaniya. (Saminu)