logo

HAUSA

CGTN Na Maraba Da Matakin Ofcom Na Amincewa Da Hakkinta Na Yada Labarai A Birtaniya

2021-04-10 16:19:13 CRI

Gidan talabijin na CGTN na kasar Sin, ya yi maraba da amincewar hukumar sa ido kan kafafen yada labarai na Birtaniya Ofcom cewa, hakkin gidan talabijin din na yada labarai a Turai na karkashin ikon Faransa, lamarin da ke ba shi damar komawa yada labarai a Birtaniya bayan dakatarwar da ya yi watanni 2 da suka gabata.

A cewar jaridar Financial Times, hukumar Ofcom ta Birtaniya, ta bayyana a jiya cewa, ta amince harkokin gudanarwar CGTN a Turai na karkashin ikon Faransa, Inda kuma yarjejeniyar yada shirye shiryen talabijin ta Turai da Birtaniyar ta rattabawa hannu, ta ba CGTN din damar komawa watsa shirye-shiryensa a kasar.

A cewar kakakin CGTN, gidan talabijin din na yabawa tare da maraba da komawar hukumomin Birtaniya kan turbar da ta dace.

Ya kara da cewa, a matsayinsa na kafar yada labarai ta kasa da kasa dake da kwarewa, CGTN na ba da rahotanni a duniya bisa gaskiya da adalci, tare kuma da inganta musaya tsakanin al’ummomin kasa da kasa da na yankuna. Haka kuma, CGTN na martabawa da kiyaye dokoki da ka’idojin kasashe da yankunan da yake aiki. (Fa’iza Mustapha)

Fa’iza Mustapha