logo

HAUSA

Sanannun mutane daga bangarori daban-daban na kasa da kasa sun bayyana adawarsu ga haramcin da aka sanyawa CGTN

2021-03-09 21:22:01 CRI

Sanannun mutane daga bangarori daban-daban na kasa da kasa sun bayyana adawarsu ga haramcin da aka sanyawa CGTN_fororder_1

Yau Talata, wasu fitattun mutane daga bangarori daban-daban na kasa da kasa, wadanda suka wallafa wani sako cikin hadin-gwiwa, a jaridar Morning Star gami da tashar intanet ta cibiyar “nuna adawa da sabon yakin cacar baka” ta kasar Birtaniya, inda suka nuna adawarsu game da haramcin da hukumar kula da harkokin sadarwar Birtaniya wato Ofcom ta sanyawa gidan talabijin na CGTN na kasar Sin. Sanannun mutanen da suka rattabawa hannu kan wannan sako sun hada da, kwararren dan jaridan kasar Australiya, kana darektan fim mai suna John Pilger, da darekan fim wanda ya samu kyautar Oscar har sau uku mai suna Oliver Stone, da sauran wasu fitattun mutane da dama.

Sakon ya nuna cewa, duk da cewa hukumar Ofcom ta ce, dalilin da ya sa ta hana kafar CGTN ci gaba da watsa shirye-shiryenta a Birtaniya, shi ne domin duk wata kafar da ta mallaki lasisin watsa shirye-shiryen rediyo a kasar, bai kamata ta gudanar da harkokinta a karkashin wata gwamnati ba. Amma gaskiyar maganar ita ce, dole ne hukumar leken asirin Birtaniya MI5 ta bincike dukkan ma’aikatan BBC, amma ba’a taba soke lasisinsu ba.

Ita kuma a nata bangaren, Fiona Edwards daga cibiyar “nuna adawa da sabon yakin cacar baka” ta ce, haramcin da gwamnatin Birtaniya ta sanya, ya zo ne a daidai lokacin da ake kara kyamar kasar Sin a karkashin jagorancin Amurka. A cewarta, sake ba wa kafar CGTN lasisin watsa shirye-shirye na da matukar muhimmanci, saboda hakan zai baiwa al’ummun Birtaniya damar kara sauraron ra’ayoyin kasar Sin.(Murtala Zhang)