logo

HAUSA

Kungiyar masanan CGTN ta ba da rahoton halin da duniya ke ciki na tinkarar cutar COVID-19

2021-07-23 11:22:28 CRI

A yau ne, kungiyar masanan CGTN ta gabatar da rahoton halin da duniya ke ciki game da yadda ake tinkarar cutar COVID-19, rahoton da ya bayyana cewa, akwai bambanci matuka ta fuskar yawan masu harbuwa da cutar da yawan mamata da kuma yawon mutane da aka yiwa allurar tsakanin kasa da kasa. Rahoton ya ce, gwamnatocin kasashe daban-daban sun taka muhimmiyar rawa a matakan kandagarki. A cikin mizani guda biyar da kungiyar ta fitar game da aikin kandagarkin cutar, Amurka na da 3 mafiya muni na gaza yakar cutar a duniya.

Wannan rahoto ya dogaro ne da alkaluman da shafukan yanar gizo na jami’ar Johns Hopkins na kasar Amurka da “Our World in Data” da na “PHARMACEUTICAL TECHNOLOGY” suka samar, tare kuma da yin la’akari da bayanan da aka bayar dangane da annoba da shawarwarin kangadarki da wasu masana a wannan fanni suka bayar, mizanan da rahoton ya gabatar, ya kunshi yawan masu harbuwa da cutar,da yawan sabbin masu harbuwa da cutar, da yawan mamata da yawan mutanen da aka yiwa alluran riga kafi, da lokacin da aka dauka wajen shawo kan cutar, inda ya jera sunayen kasashe 51 bisa alkaluman da aka bayar kafin ran 14 ga watan Yuli, don bayyana halin da kasa da kasa ke ciki wajen tinkarar cutar da kuma ci gaba da suke samu.

Rahoton na nuna cewa, Amurka na fuskantar mummunan yanayi a halin yanzu, yayin da kasashen Brazil da Indiya da Birtaniya da Faransa ke biye mata baya. Yawan masu harbuwa da cutar a kasar ya haura miliyan 34 yayin da yawan mamata ya kai fiye da dubu 600, wanda ke kan gaba a duniya. Ban da wannan kuma, kwanaki 62 ne kawai da Amurka ta samu yawan masu karbuwa da cutar da bai wuce 5000 a rana ba tun barkewar cutar, abin da yake nuna cewa, Amurka tana cikin mawuyacin hali. (Amina Xu)