logo

HAUSA

Zhao Lijian: Bukatar bincikar cibiyar Fort Detrick ta yi daidai da kiraye kirayen al’ummun duniya

2021-07-21 20:01:20 CRI

Zhao Lijian: Bukatar bincikar cibiyar Fort Detrick ta yi daidai da kiraye kirayen al’ummun duniya_fororder_德特里克堡

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Zhao Lijian, ya ce bukatar bincikar cibiyar gwaje gwaje ta Fort Detrick dake Amurka, da wasu sassan kasa da kasa ciki har da Sin suka gabatar, ta yi daidai da kiraye kirayen da al’ummun duniya ke yi, don haka kamata ya yi Amurka ta amsa wannan kira, ta yadda hakan zai taimaka a kai ga cimma nasarar binciken asalin kwayar cutar numfashi ta COVID-19 da ake yi.

Zhao Lijian ya yi wannan tsokaci ne, yayin taron manema labarai na Larabar nan, yana mai cewa, budaddiyar wasikar da aka gabatarwa hukumar lafiya ta duniya WHO, ya zuwa yammacin yau ta samu sa hannun Sinawa kimanin miliyan 5. (Saminu)

Saminu