logo

HAUSA

Yin hadin gwiwa a fannin fasahar zamani ita ce hanya kadai mafi dacewa

2021-07-19 18:16:45 CMG

Yin hadin gwiwa a fannin fasahar zamani ita ce hanya kadai mafi dacewa_fororder_11

A ranar Juma’a da ta gabata, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya yi jawabi a kwarya-kwayar taron shugabannin kungiyar hadin gwiwar tattalin arzikin kasashen Asiya da tekun Pacific (APEC), inda ya ce tsarin tattalin arziki mai alaka da fasahar zamani na kasashe daban daban a hade suke, don haka yin hadin gwiwa a wannan fanni, ita ce hanya kadai da ta dace, yayin da yunkurin magance hadin kai da mai da wani saniyar ware, babu abin da zai haifar, sai lalata tsarin tattalin arzikin. Shugaba Xi ya fadi haka ne, a matsayin suka kan kura-kuran da wata kasa ta aikata, gami da shawara game da dunkulewar kasashe daban daban a fannin tattalin arziki mai alaka da fasahohi na zamani, musamman ma wanda ya shafi na’ura mai kwakwalwa ta kamfuta, da yanar gizo ta Internet.

Yunkurin magance hadin gwiwa, na daga cikin matakan da kasar Amurka ta dauka. A kokarin Amurka na ganin an hana tasowar kasar Sin ta girgiza matsayinta na babakere a duniya, kasar Amurka ta dade tana kokarin hana fitar da fasahohin zamani zuwa kasar Sin. Yayin da yake halartar taron kungiyar APEC a wannan karo, shugaban kasar Amurka Joe Biden, shi ma yana kokarin neman kafa wasu ka’idojin ciniki a fannin fasahohin zamani a yankin Asiya da Pacific, wadanda ba su sanya kasar Sin a ciki ba. Sai dai Mista Biden bai yi nasarar cimma burinsa ba, ganin yadda wasu kasashen yankin ba su yarda da hakan ba.

Saboda yadda kasar Amurka ta saba yin babakere da nuna fin karfi a duniya, don haka duk lokacin da wata kasar ta iya takara da ita, ta kan ta da rikici da yin fito-na-fito da ita, maimakon neman damar gudanar da cikakken shawarwari da hadin gwiwa. Idan ba mu manta ba, a shekarun 1980, kasar Japan ta samu damar tasowa cikin sauri a fannin kananan na’urorin hada kayayyaki na zamani da ake kira “Semiconductor”, har ta yi takara da kasar Amurka sosai. Lamarin ya sa kasar Amurka ta yi amfani da dalili na wai cewa “kasar Japan na satan fasahohin Amurka”, inda ta tilasta Japan sa hannu kan wata yarjejeniyar takaita fasahohin zamani na kasar, ta yadda kasar Japan ta rasa yawancin kasonta a kasuwannin duniya, da damar yin takara da kasar Amurka.

Yadda kasar Amurka ta samu nasarar hana tasowar kasar Japan a baya, ya sa take neman daukar makamancin wannan mataki don hana kasar Sin samun ci gaba ta fuskar fasahohi na zamani, sai dai Amurka a wannan karo, ba ta lura da yadda yanayin zamani ya sauya sosai ba.

Me ya sa shugaba Xi Jinping ya ce yunkurin yin babakere da mai da wata kasa saniyar ware ba zai haifar da da mai ido ba?

Da farko, matakin ya saba wa yanayin dunkulewar kasashe daban daban waje guda.

Bayan yanayin dunkulewar kasashe karo na farko a lokacin mulkin mallaka, da na biyu wanda manyan kamfanonin kasa da kasa suke jagoranta, yanzu muna cikin lokacin dunkulewar kasashe karo na 3 da tattalin arizki mai alaka da fasahohin zamani ke jagoranta. Inda ta hanyar wayoyin salula na zamani ake hada daidaikun mutane da yanar gizo ta Internet, kana fasahar sadarwa ta 5G za ta wanzar da hadewar mutum da na’ura, da kayayyaki. Wadannan fasahohi za su taimaka wajen tabbatar da hadewar dukkan mutane da kayayyaki na duniyarmu, maimakon rarrabuwa cikin bangarori daban daban. A sakamakon wannan yanayin da muke ciki ne, ya sa kasar Sin ke kokarin ba da taimako a fannin cudanyar sassa daban daban na duniya, ta hanyar shawarar “ Ziri Daya da Hanya Daya”, duk da cewa kasar Amurka a nata bangare tana kokarin kafa wasu tsirarun kungiyoyi, karkashin jagorancinta.

Na biyu shi ne, kasar Amurka ba ta kimanta karfin kasar Sin cikin daidai ba.

Alkaluman da aka samu sun nuna cewa, darajar tattalin arziki mai alaka da fasahohin zamani na kasar Sin ta zarce dalar Amurka triliyan 6 a shekarar 2020, wadda ta kasance mafi yawa na biyu a duniya. Kana yawan darajar a cikin GDPn kasar Sin ya haura daga kashi 10% na shekarar 2002 zuwa kashi 38.6% na shekarar 2020. Zuwa karshen shekarar 2020, yawan mutanen kasar Sin da suke yin amfani da yanar gizo ta Internet ya karu zuwa miliyan 989, jimillar da ta kai kashi 70.4% na daukacin al’ummar kasar. A sa’i daya, ana kokarin raya fasahar sadarwa ta 5G. Ya zuwa karshen watan Maris na shekarar 2021, an kafa tashoshin 5G dubu 819 a kasar Sin, wadanda suka zama wani bangare na tsarin yanar gizo na 5G mafi girma a duniya. Kana a fannin kasuwanci ta yanar gizo ta Internet, darajar kasuwar kasar Sin ta kai dalar Amurka triliyan 1.18, wadda ta ninka darajar kasuwannin kasar Amurka har fiye da sau 3. Tushen tasowar kasar Sin a fannin tattalin arziki mai alaka da fasahohin zamani shi ne nagartattun manufofin da gwamnati ta dauka, da yadda mutanen kasar suke dogaro da kai wajen kirkiro sabbin fasahohi, gami da dimbin bukatun da ake samu a kasuwannin gidan kasar, don haka ba zai yiwu ba a samu hana tasowar kasar bisa wani matakin da kasar Amurka ta dauka. Kana a idanun sauran kasashe, kasar Sin ita ce mai samar da fasahohi da jari, da tsarin ciniki, gami da manyan kasuwanni, saboda haka dunkulewar tattalin arzikin duniya a fannin fasahohin zamani ba za ta iya magance rawar da kasar Sin ke takawa ba.

Ko da yake kasar Sin tana sahun gaba a duniya a fannin tattalin arziki mai alaka da fasahohin zamani, amma ba kamar yadda kasar Amurka take tsumulmular raba fasahohi ba, kasar Sin tana kokarin hadin gwiwa da sauran kasashe, tare da raba fasahohi da su. Dalilin da ya sa haka shi ne domin kasar Sin ba ta da girman kai, ba kamar yadda kasar Amurka take kallon kanta a matsayin “ kasa mafi karfi a duniya” , tare da kokarin yin babakere a duniya ba. Kasar Sin tana kokarin raya fasahohi ne don wadatar da kai, gami da samar da gudunmowa ga daukacin dan Adam masu makomar bai daya, inda a ganin kasar Sin, samun wata duniya mai zaman lafiya, da walwala, da al’adu iri-iri, shi ma zai haifar da moriya ga ita kanta. Saboda haka kasar Sin na rungumar manufar “koya wa mutum fasahar kamun kifi ya fi ba shi kifi kai tsaye”, yayin da take hadin gwiwa da sauran kasashe a fannin fasahohin zamani, musamman ma da kasashen Afirka. Yanzu haka kasashen Afirka su ma suna samun ci gaba cikin sauri a bangaren tattalin arziki mai alaka da fasahohin zamani, inda tabbas kasar Sin za ta iya samar da taimako da gudunmowa sosai. (Bello Wang)

Bello