logo

HAUSA

Sin Ta Yi Kira Ga WHO Da Ta Yi Watsi Da Siyasantar Da Batun Gano Asalin Cutar COVID-19

2021-07-19 19:59:50 CRI

Sin Ta Yi Kira Ga WHO Da Ta Yi Watsi Da Siyasantar Da Batun Gano Asalin Cutar COVID-19_fororder_sin

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Zhao Lijian, ya ce Sin na fatan hukumar lafiya ta duniya WHO, za ta ci gaba da aiwatar da matakan gano asalin kwayar cutar numfashi ta COVID-19, bisa kwarewar masana kimiyya, ta kuma yi watsi da yunkurin wasu sassa na siyasantar da batun, a wannan gaba da hukumar ke shiga zagaye na 2 na aikin binciken.

A ranarJumma’ar karshen makon jiya ne dai WHOn ta kaddamar da zagaye na biyu, na binciken asalin kwayar cutar a kasar Sin, tana mai kira ga mahukuntan kasar da su samar da yanayi na fayyace komai, da rungumar hadin gwiwar masana don cimma nasarar aikin.

Game da hakan, Zhao Lijian ya shaidawa taron manema labarai na yau Litinin cewa, matsayin kasar Sin ya yi daidai da na kasashe da dama, cewa binciken asalin kwayar cutar COVID-19 aiki ne na kimiyya, wanda ke bukatar hadin kan masana na sassan duniya. A hannu guda kuma, ya yi tir da matakin wasu kasashe kalilan, ciki har da Amurka, bisa yunkurin su na siyasantar da lamarin.

Wani binciken jin ra’ayin jama’a da mujallar “Global Times” ta gudanar, ya nuna cewa, kaso sama da 90 bisa dari na wadanda aka zanta da su, na ganin kamata ya yi a karkata zango na 2 na wannan bincike zuwa Amurka, wato a binciki cibiyar gwaje gwaje ta “Fort Detrick” dake jihar Maryland.

Ya zuwa yammacin yau Litinin, Sinawa sama da 750,000 sun sanya hannu kan wata budaddiyar wasika da aka aikewa WHO, suna masu bukatar hukumar ta gudanar da binciken kimiyya, a waccan cibiyar gwaje gwaje dake Amurka.

Don haka ne ma Zhao ke cewa, ya kamata Amurka ta saurari ra’ayoyin al’ummun kasa da kasa ciki har da Sinawa, ta kuma gabatar da cikakken martani don gane da waccan wasika, da kuma sakamakon jin ra’ayin al’umma da aka gudanar.  (Saminu)

Saminu