logo

HAUSA

Ya Zama Wajibi A Mai Da Hankali Kan Gano Asalin Annobar COVID-19 A Amurka A Mataki Na 2

2021-07-20 21:18:17 CRI

Ya Zama Wajibi A Mai Da Hankali Kan Gano Asalin Annobar COVID-19 A Amurka A Mataki Na 2_fororder_annoba

Kwanan baya, hukumar lafiya ta duniya wato WHO, ta gabatar da shirin aikinta na gano asalin kwayar cutar numfashi ta COVID-19 a mataki na biyu, ko da yake hakan bai yi daidai da matsayin kasar Sin da na kasashen duniya da yawa kan batun ba. Yanzu haka kuma, kasashe 55 sun mika wa WHO wasikar adawa da siyasantar da batun gano asalin cutar COVID-19, tare da yin kira da a rungumar kimiyya a kan batun.

Kasar Sin, kasa ce ta farko da ta sanar wa WHO barkewar annobar COVID-19. Kana kuma ta samar da yanayi na fayyace komai kan batun gano asalin annobar, ta kuma riga ta gayyaci masanan WHO zuwa kasar har sau biyu, inda wasu masanan suka nuna cewa, sun je duk wurin da suke son zuwa, tare da yin hira da duk wanda suke son yin hira da shi.

A ranar 30 ga watan Maris, bayan da kungiyar bincike ta hadin gwiwar WHO da Sin, ta kammala aikinta a kasar Sin dangane da gano asalin annobar a duniya, ta kuma kaddamar da wani rahoto a hukumance, inda a cewarta, ba zai yiwu annobar ta COVID-19 ta bulla daga dakin gwajin kasar Sin ba.

Don haka dai, ya zama wajibi a mai da hankali kan gano asalin annobar a kasar Amurka a mataki na biyu, kasancewarta ta fi gazawa wajen yaki da annobar. Ya zuwa yanzu ana nuna shakku a fannoni da dama, kan yadda Amurka take yaki da annobar, kasancewar kasar na samun masu adadi mafi yawa na masu kamuwa da annobar a duniya, kuma adadin wadanda suka rasu sakamakon annobar a Amurka ya dara na sauran yankunan duniya.

Har zuwa yanzu, Amurka ba ta amsa tambayar kasashen duniya ba tukuna, wato me ya sa aka rufe dakin gwaji na Fort Detrick a watan Yulin shekarar 2019 ba zato ba tsammani, wanda shi ne sansanin nazarin makamai masu guba, da makaman halitta mafi girma a Amurka?

Da batun ko rufewar dakin gwajin na da nasaba da barkewar wani nau’in ciwon numfashi a wasu sassan Amurka, da samun dimbin mutanen da suka kamu da ciwon sigarin latirori?

A watan Maris na shekarar bara, Robert Redfield, tsohon darektan cibiyar dakilewa, da kandagarkin cututtuka ta Amurka ya amince da cewa, wasu mutane sun rasa rayukansu ne sakamakon kamuwa da annobar COVID-19, a maimakon cutar mura da ta barke a watan Satumban shekarar 2019. A watan Yunin bana kuma, kwalejin nazarin kiwon lafiya na Amurka, ya kaddamar da wani rahoton nazari da ke cewa, a watan Disamban shekarar 2019 ne annobar ta COVID-19 ta fara bazuwa a Amurka.

Sakamakon karuwar shakku da ake nunawa Amurka, ya sa karin kasashe suka yi kira gare ta, da ta amince a binciki asalin annobar COVID-19 a cikin yankunan ta. Wadannan kasashe sun yi wannan kira ne domin rungumar adalci da gaskiya da kimiyya, tare da yin adawa da sanya siyasa cikin batun gano asalin annobar COVID-19. Ana ganin cewa, idan ba za a yi binciken asalin annobar a Amurka ba, sai a kasar Sin kadai, to mene ne ma’anar kimiyya? Kana idan WHO ba za ta yi adalci kan batun ba, to mene ne ma’anar aikinta na gano asalin annobar? (Tasallah Yuan)

Tasallah Yuan