logo

HAUSA

An Yi Ba’a Kan Yadda Wasu Kasashen Yammacin Duniya Suka Yi Karya Bisa Binciken Ra’ayoyin Jama’a

2021-07-19 21:11:35 CRI

An Yi Ba’a Kan Yadda Wasu Kasashen Yammacin Duniya Suka Yi Karya Bisa Binciken Ra’ayoyin Jama’a_fororder_amurka

Shahararriyar kafar yada labaru ta kasar Amurka wato Bloomberg News, da hukumar binciken ra’ayoyin jama’a ta Pew, sun kaddamar da sakamakon bincike guda 2 na jin ra’ayoyin jama’a a kwanan baya, inda a cewarsu, Amurka ta fi yaki da annobar cutar COVID-19 a duniya, kuma kimar kasar Sin a idon duniya ba ta da kyau, yayin da kimar Amurka ta farfado. Kamar yadda ake zato, akasarin ra’ayoyin jama’a sun yi ba’a kan sakamakon.

Bloomberg News, kamfani ne mafi girma a duniya a fannin watsa labarun hada-hadar kudi, wanda yake kiran kansa mai watsa labaru cikin adalci. Hukumar Pew kuwa, hukuma ce mai zaman kanta a idon duniya. Amma sakamakon binciken ra’ayoyin jama’a da suka kaddamar ya bata sunansu kwata kwata.

Bloomberg News ya gyara ka’idar ba da maki, a karshe dai ta mayar da Amurka a matsayin wadda ta fi yaki da annobar a duniya, lamarin da ya sanya kasashen duniya suka sossoke shi da cewa, ba shi da kunya.

Hukumar Pew kuma, ta gudanar da binciken ra’ayoyin jama’ar ne a kasashe da yankuna 17 masu karfin tattalin arziki kawai, a karshe dai ta yanke hukuncin cewa, kimar kasar Sin a idon yawancin mutane ba ta da kyau. Ana mamakin cewa, me ya sa hukumar ta Pew ba ta gudanar da binciken a kasashen Asiya, Afirka da Latin Amurka ba? Ko kasashe da yankuna 17 za su iya wakiltar kasashe fiye da 190 mambobin MDD?

Bloomberg News da hukumar Pew, suna kiran kansu masu kwarewa a ayyukansu kuma masu zaman kansu. Amma hakika dai su wani bangare ne kawai na yakin Amurka ta fuskar akasarin ra’ayoyin jama’a. Sun kuma yi dabaru ne domin tabbatar da odar Amurka.

Mene ne ma’anar odar Amurka? Amurka na gaya wa kasashen duniya cewa, kada su yi abin da take yi, maimakon haka su yi abin da ta gaya musu su yi. George Koo, wanda ya kafa kamfanin kawancen manyan tsare-tsaren duniya na Amurka, ya ba da sharhi a kwanan baya cewa, odar kasa da kasa ba odar Amurka ba ce. Amma wasu kafofin yada labaru da hukumomi na Amurka, suna kokarin tabbatar da odar Amurka. Ba su san cewa, suna kara kokarinsu ne kawai, amma kuma kasashen duniya suna kara yi musu ba’a, suna kuma kara bata sunan su da kan su. (Tasallah Yuan)

Tasallah Yuan