logo

HAUSA

Amurka Ta Kitsa Karya Kan Masu Satar Shiga Yanar Gizo Na Kasar Sin

2021-07-21 21:09:43 CRI

Amurka Ta Kitsa Karya Kan Masu Satar Shiga Yanar Gizo Na Kasar Sin_fororder_amurka

Kwanan baya, kasar Amurka ta hada kai da wasu kawayenta na yammacin duniya, inda suka fitar da wata sanarwa, dake cewa kasar Sin ta kai hari kan yanar gizon Amurka. Haka kuma Amurka ta gabatar da kara kan wasu Sinawa su 4, wadanda ta zarga da laifin wai sun saci bayanai a yanar gizon ta. To sai dai kuma Amurka ta fayyace shaidun ta a fili ba. Don haka zargin da ta yi wa kasar Sin ba shi da kan gado, ta kuma mayar da fari baki kawai. Ba ta ji kunya ba, inda ta sake kitsa wata karya ta daban. Kamar dai yadda bahaushe kan ce “Gwano baya jin warin jikinsa”.

Ko shakka ba bu, Amurka ce ta fi yawan masu satar shiga yanar gizo a duniya. Tun can da Amurka ta nuna fifiko ta fuskar fasahar tsaro a yanar gizo, ba ta jin tsoron komai, inda ta rika yin leken asiri kan kawayenta, da abokan gabarta a sassa da yawa na duniya, ta kuma saci manyan bayanan sauran kasashe, da kuma bayanan sirri da suka shafi rayuwar mutane. Kasashen duniya na kara fahimtar cewa, lallai Amurka, ta fi yin barna kan tsaron yanar gizon duniya.

Wani shahararren kamfanin kula da tsaron yanar gizo na kasar Sin ya bayyana cikin rahotonsa cewa, kungiyar APT-C-39 karkashin shugabancin hukumar leken asiri ta CIA ta Amurka, ta taba daukar shekaru 11 tana kai hari a yanar gizon hukumomin sararin samaniya na kasar Sin, da masana’antun hakar man fetur, da manyan kamfanonin yanar gizo, da hukumomin gwamnatin kasar Sin, lamarin da ya gurgunta tsaron kasar Sin, da muradunta ta fuskar tattalin arziki.

Amurka ba za ta iya boye gaskiya ba. Ita ce kasar da ta fi kai wa kasar Sin hari ta yanar gizo. Amma yanzu ta dora wa kasar Sin laifin kai hari a yanar gizo. Lallai Gwano baya jin warin jikinsa.

Abun da Amurka ta yi ya kara sanya kasashen duniya kara gane cewa, Amurka da kawayenta na yammacin duniya, suna yin dabaru sosai, domin kiyayewa, da inganta yin danniya a yanar gizo, da abubuwa na rashin kunya da suke yi. (Tasallah Yuan)

Tasallah Yuan