logo

HAUSA

Sin: Shawo kan kalubalen sauyin yanayi aiki ne na hadin gwiwar dukkanin sassa

2021-07-21 20:10:44 CRI

Sin: Shawo kan kalubalen sauyin yanayi aiki ne na hadin gwiwar dukkanin sassa_fororder_赵立坚

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Sin Zhao Lijian, ya ce Sin na fatan Amurka za ta fahimci cewa, shawo kan kalubalen sauyin yanayi aiki ne na hadin gwiwar dukkanin sassa, kuma kamata ya yi ta yi aiki tare da masu ruwa da tsaki, don kafa misali a fannin ayyukan hadin gwiwar kasa da kasa. 

Da yake tsokaci a yau, don game da kalaman da wakilin kasar Amurka a fannin sauyin yanayi John Kerry ya yi a ranar Litinin, cewa ya dace Sin ta yi hadin gwiwa da Amurka wajen rage hayaki mai gurbata muhalli, Zhao ya ce Sin, kasa mai tasowa ce mafi girma a duniya, yayin da Amurka ita ce kasa mai sukuni mafi girma a duniya, don haka ya dace su ci gaba da cudanya, da inganta tattaunawa kan tsare tsare a wannan fanni. 

Jami’in ya kara da cewa, bai dace Amurka ta rika kutsawa cikin harkokin cikin gidan Sin, tana kokarin gurgunta moriyar Sin ba, a hannu guda kuma ta nemi hadin kan ta cikin harkokin da suka shafi sassan biyu, ko wadanda suka shafi duniya baki daya.

Zhao ya kara da cewa, har kullum Sin za ta ci gaba da dora muhimmancin gaske, ga tabbatar da ganin yawan hayaki mai dumama yanayin duniyarmu da za ta fitar ya kai matsayin koli kafin shekarar 2030, da kuma kokarin samun daidaito tsakanin yawan hayakin da za ta fitar, da yawan abubuwan da za su shawo kan hayakin kafin shekarar 2060. (Saminu)

Saminu