logo

HAUSA

Hayaki ba ya buya ko a gidan mai rowa

2021-07-21 19:30:40 CMG

Hayaki ba ya buya ko a gidan mai rowa_fororder_微信图片_20210721191558

A farkon wannan shekara ce, tawagar masana ta kasa da kasa ta kawo ziyara kasar Sin kamar yadda hukumar lafiya ta duniya ta bukata, don gudanar da aikin binciken gano asalin kwayar cutar COVID-19, inda tawagar tare da taimakon takwararta ta kasar Sin, suka ziyarci sassa daban-daban na birnin Wuhan. Wannan tawaga ta kammala aikinta har an fitar da sakamako da duniya ta yi na’am da shi.

Sai dai wani abin mamaki shi ne, a kwanakin baya babban darektan hukumar lafiya ta duniya (WHO) Tedros Adhanom Ghebreyesus, ya bayyana cewa, wai saboda karancin bayanai na zahiri a farkon barkewar annobar COVID-19, ya sa aikin binciken gano asalin kwayar a kasar Sin ya gamu da cikas.

Amma duniya ta san cewa, yayin ziyarar tawagar kwararru a kasar Sin, kasar Sin ta gabatar mata dukkan muhimman bayanai da suke bukata daya bayan daya, haka kuma tawagar masanan ta ziyarci cibiyoyin kandagarki da dakile yaduwar cututtuka dake Hubei, da Wuhan, da cibiyar nazarin kwayoyin cututtuka ta Wuhan da sauran hukumomi, da dakunan bincike daban-daban, sun kuma yi musayar bayanai na kimiyya da masana daga hukumomin da abin ya shafa. Bayan wuraren da suka ziyarta da kara fahimtar abubuwa, tawagar masanan ta amince cewa, tunanin da ake cewa, wai cutar ta bulla ne daga dakin bincike, ba zai taba yiwuwa ba. Abubuwa da aka zayyana a bayyane su ke, kuma an gabatar su a rahoton aikin binciken gano asalin cutar na hadin gwiwa da WHO ta fitar a hukumance a cikin watan Maris na wannan shekara. Don haka, bayanan babban darektan WHO, tamkar wani yunkuri na mayar da hannun agogo baya. Kuma ba a sauyawa tuwo suna.

Duk wani batu da ya shafi COVID-19, kama daga aikin binciken gano asalin kwayar cutar, da matakan kandagarki, da alluran riga kafinta, duk ayyuka ne na kimiya. Amma matakan da wasu tsirarun kasashen yamma da ‘yan korensu ke yi na neman siyasantar da batun ko neman dorawa wata kasa laifi, ko bata mata suna, ba zai taba haifar da da mai ido ba. Koda a baya-bayan nan, wasu masana sun fito fili sun karyata tunanin da wasu ke yi na yiwuwar bullar cutar daga wani dakin gwaji, amma har yanzu kasar Amurka na neman karyata bayanai da binciken masana, alhali ba ta bari an gudanar da irin sahihin binciken gano asalin kwayar cutar da aka gudanar a kasar Sin ba. Komai aka yi da Jaki, ai sai ya ci Kara.

Wani abin takaici shi ne, yadda kamfanin dillancin labarai na Bloomberg na kasar Amurka, ya wallafa jerin kasashen dake kan gaba wajen yakar annobar COVID-19, inda ya sanya Amurka a matakin farko. Wai kasar da ta gaza shawo kan cutar, da ma hana gudanar da binciken gano asalinta cutar a cikin kasarta, ita ce ta wuce kasashe irinsa kamar kasar Sin da suka yi amfani da shawarwari da matakai na kimiya wajen yakar cutar. Wannan ya kara nuna halayyar Amurka na zama nahainiya mai canza launi, Yau ta ce wannan, gobe kuma ta fadi wani abu daban. Dokin mai baki, ya fi Gudu.

Masu fashin baki na jaddada cewa, dole ne a martaba dalilan kimiyya na zahiri game da aikin. A hannu guda kuma, watsi da sakamakon da aka fitar cikin rahoton kwararrun Sin da WHO, tare da yin kira da a sake gudanar da binciken a Sin a karo na 2, ba hanya ce sahihiya da za ta bayar da sakamako mai kyau ba, sai dai kawai share hanya ga masu amfani da batun, wajen cimma munanan muradun siyasa. Wanda ya yi nisa ba ya jin kira. (Ibrahim Yaya)

Ibrahim