logo

HAUSA

Peng Liyuan Ta Gabatar Da Jawabi Ga Taron Dandalin SCO Dangane Da Ilmantar Da Mata Da Yaki Da Fatara

2021-07-20 20:16:48 CRI

Peng Liyuan Ta Gabatar Da Jawabi Ga Taron Dandalin SCO Dangane Da Ilmantar Da Mata Da Yaki Da Fatara_fororder_peng

Mai dakin shugaban kasar Sin Peng Liyuan, ta gabatar da jawabi ta kafar bidiyo, ga mahalarta taron dandalin da kungiyar hadin gwiwa ta Shanghai ko SCO a takaice, ta shirya don gane da ilmantar da mata da yaki da talauci.

Peng Liyuan, wadda ta gabatar da jawabin a Talatar nan, ta ce yaki da talauci, da samun farin ciki akidu ne na mata. Kuma ta hanyar samun ilimi, da wayewa da sana’o’i, mata na samun zarafin fitar da kawunan su daga kangin talauci.

Ta ce ya zama wajibi a jinjina wa kwazon kasar Sin, wanda ya kai ta ga samun cikakkun nasarori a fannin yaki da talauci, tare da tsame miliyoyin mata Sinawa daga fatara. Uwar gidan shugaban na Sin ta kara da cewa, mahukuntan lardin Guizhou sun aiwatar da shirin raya masana’antun sana’ar hannu tsakanin mata, wanda ya tallafawa sama da mata 500,000 samun guraben ayyukan yi a gidajen su. Karkashin tallafin wani shiri da aka yi wa lakabi da “Spring Bud”, sama da ‘yan mata miliyan 3 dake fama da talauci sun kai ga kammala karatu, tare da shiga sahun shekarun girman su cike da kuzari. Har ila yau madam Peng Liyuan ta buga misali da wata malama mai suna Zhang Guimei, wadda ta yi shekaru fiye da 40 a yankin tsaunuka da ke fama da talauci. Ta dauki nauyin kafa makarantar sakandare kyauta ga ‘yan mata, ta kai ga tallafawa yara mata 2,000 cika burin su na shiga jami’a. Madam Peng Liyuan ta ce, irin wadannan labarai ne masu faruwa yau da kullum a kasar Sin.

Daga nan sai mai dakin shugaban kasar Sin ta bayyana burin hada karfi da karfi, wajen nunawa juna kauna, da zurfafa hadin gwiwa a fannonin ilmantar da mata da rage fatara, ta yadda ilimi zai farfado da burin mata, zai kuma baiwa karin mata damar inganta rayuwar su.  (Saminu)

Tasallah Yuan