logo

HAUSA

Sin ta samar da alluran rigakafin cutar COVID-19 biliyan 5 cikin shekara daya

2021-07-16 14:19:18 CRI

Sin ta samar da alluran rigakafin cutar COVID-19 biliyan 5 cikin shekara daya_fororder_hoto2

Yau Jumma’a, babban injiniya na ma’aikatar harkokin masana’antu da sadarwa ta kasar Sin Tian Yulong ya bayyana cewa, ma’aikatar ta jagoranci kamfanonin kasar Sin wajen gaggauta aikin samar da alluran rigakafi, domin biyan bukatun al’ummomin kasar. Ya zuwa yanzu, kasar Sin ta samar da alluran rigakafin cutar COVID-19 biliyan 5 cikin shekara daya, kuma, gaba daya, an samar wa al’ummomin kasar alluran rigakafin biliyan 1.4, yayin da aka samar wa kasashen ketare alluran rigakafin miliyan 570.

Ya ce, fasahohin sarrafa alluran rigakafin suna da wuya, kuma akwai ayyuka da yawa da abin ya shafa. Ma’aikatar harkokin masana’antu da sadarwa ta dukufa wajen inganta ayyukan samar da alluran rigakafi, domin tabbatar da ingancin alluran da kuma samar da su cikin sauri. Ya ce cikin karshen rabin shekarar bana, ma’aikatar za ta bada goyon baya ga kamfanonin sarrafa alluran rigakafin cutar COVID-19 na kasar Sin don su habaka hadin gwiwarsu da kamfanonin kasa da kasa ta hanyoyi daban daban, ta yadda za a biya bukatun al’ummomin kasa da kasa. (Maryam)