"Shirin Kasar Sin" Yana Karfafa Gwiwa Kan Yaki Da Annobar COVID-19 Da Farfadowar Tattalin Arziki A Yankin Asiya Da Fasifik
2021-07-17 17:12:12 cri
Lokacin da yake halartar kwarya-kwaryar taro na shugabannin APEC ta kafar bidiyo a jiya Jumma’a, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar da muhimman shawarwari guda hudu game da inganta hadin gwiwar yaki da annobar COVID-19 da farfadowar tattalin arziki a yankin Asiya da Fasifik, wadanda suka samu yabo da amincewa sosai daga wajen bangarori daban daban. Ronnie Lins, darektan cibiyar nazarin harkokin kasar Sin na kasar Brazil, kuma masanin tattalin arziki, ya yi imanin cewa jawabin na shugaba Xi Jinping ya samar da wata mafita ga kasashen duniya don yaki da annobar tare da inganta farfadowar tattalin arziki, wanda ke da matukar muhimmanci.
A yayin taron kolin APEC, shugaba Xi Jinping ya jaddada matsayin kasar Sin da matakan da za ta dauka wajen goyon bayan kasashen duniya a fannin yaki da annobar, ciki har da ba da tallafin kudi na dala biliyan 3 don taimakawa kasashe masu tasowa a cikin shekaru uku masu zuwa, da kuma bada goyon baya ga samu shaidar ‘yancin mallakar fasaha ta alluran riga-kafin COVID-19. Bugu da kari, kasar Sin a shirye take ta shiga a dama da ita cikin ayyukan hadin gwiwa kamar tabbatar da tsaron tsarin samar da alluran riga-kafi da inganta jigilar muhimman kayayyakin da dai sauransu.
Domin inganta yankin Asiya da Pasifik wajen kawar da mummunan tasirin da annobar ta yi tun da wuri, da komawa kan hanyar ci gaba yadda ya kamata, shugaba Xi Jinping ya gabatar da muhimman shawarwarin da suka hada da; “zurfafa dunkulewar tattalin arzikin yankin", da “nacewa ga neman dauwamamman ci gaba dake iya hada kowa da kowa”, da “amfani da damar yin kirkire-kirkire kan fasaha ", wanda ke nuna goyon bayan da ko da yaushe kasar Sin ke bayarwa kan dunkulewar tattalin arzikin shiyyar da dunkulewar tattalin arzikin duniya, wadda kuma ke samar da sabuwar hanyar farfado da tattalin arzikin duniya baki daya. (Bilkisu Xin)