logo

HAUSA

Sin da Masar za su baiwa Palasdinawa dake zirin Gaza gudummawar alluran riga kafin COVID-19

2021-07-19 10:49:53 CRI

Sin da Masar za su baiwa Palasdinawa dake zirin Gaza gudummawar alluran riga kafin COVID-19_fororder_0719-Ibrahim4-Gaza

Kasashen Sin da Masar, jiya Lahadi sun yanke shawarar baiwa Palasdinawan dake zaune a zirin Gaza gudummawar alluran riga kafin COVID-19 dubu 500, a wani mataki na magance bukatun gaggawa na mazauna wurin.

Wannan sanarwa na zuwa ne, yayin da dan majalisar gudanarwar kasar Sin, kana ministan harkokin wajen kasar Wang Yi, ya gana da takwaransa na kasar Masar Sameh Shoukry, yayin ziyarar da Wang Yi ya kai garin Alamein dake gabar ruwa a arewacin kasar ta Masar.

Kasashen biyu dai suna bibiyar halin da ake ciki, biyo bayan barkewar tashin hankali na baya-bayan nan tsakanin Isra’ila da Palasdinu. Sun jaddada cewa, yayin da ake ci gaba da kokarin magance batun Palasdinu, kamata ya yi kasashen duniya su nuna damuwa game da yanayin jin kai da al’ummar Palasdinawa ke ciki, musamman daukar matakan da suka dace, don taimakawa mazauna wurin yakar COVID-19.

Za dai a samar da alluran da ake shirin baiwa Palasdinawan ne, a kamfanin hada alluran da kasashen biyu suka kafa tare a kasar Masar, daga bisani kuma, a aika su nan da nan bisa tsarin da aka cimma da bangaren Palasdinawa. (Ibrahim)