logo

HAUSA

Masanan Kimiyya: Babu Yiwuwar Bil-Adam Ne Ya Kirkiro Cutar COVID-19

2021-07-16 20:15:44 CRI

Masanan Kimiyya: Babu Yiwuwar Bil-Adam Ne Ya Kirkiro Cutar COVID-19_fororder_a686c9177f3e67096ad4c49c3ea3fe3bf9dc5563

BY CRI Hausa

Masanan kimiyya 21 na kasar Sin da wani masani na Birtaniya dake aiki a nan kasar Sin, sun fitar da wani bayani na hadin gwiwa a yau Juma’a, inda suka ba da shaidu bisa nazarin da suka yi cewa cutar COVID-19 ta samo asali ne daga Indalahhi babu yiwuwar cewa, dan-Adam ne ya kirkiro ta.

Ra’ayin wannan bayani mai taken “Shaidu kan asalin kwayar cutar SARS-CoV-2” na samun karbuwa da amincewa daga bangarori daban-daban, marubuci na farko Wu Zhongyi, farfesa a kwalejin nazarin kimiyyar hallitu na jami’ar Sun Yat-sen, ya bayyana cewa, wani ra’ayi daga tunanin sauyawar halittu zuwa wani abu mai inganci ya samu karbuwa matuka daga jama’a wato, sauyawar halittu babu wani dalili na musamman, idan aka dauki muhallin halittu a matsayin mai hada agogo, to ba shakka zai zama makaho mai hada agogo. Ba wanda zai iya kirkiro wani abu dake iya dacewa da muhalli sosai cikin gajeren lokaci, ana bukatar sauye-sauye da dama na dogon lokaci.

Saboda haka, ya bayyana cewa, wadannan masana sun gano cewa, kafin barkewar annobar COVID-19, cutar ta dade tana yaduwa tsakanin namun daji da Bil Adama, kuma sannu a hankali ta rika sauyawa har ta samu damar dacewa da jikin Bil Adama. Wannan ya sa cutar take kokarin sauya yanayinta ta yadda za ta rika saurin yaduwa tsakanin Bil Adama. (Amina Xu)