logo

HAUSA

Hankaka mai da Dan wani Naka

2021-02-03 21:27:50 CRI

Hankaka mai da Dan wani Naka_fororder_202102003-sharhi-Ibrahim

A duk lokacin da aka ambaci batun dan kasa, ana nufin wanda aka haifa a kasa, mace ne ko namiji, ko wanda ya samu iznin zama a wata kasa a hukumance, ko bisa radin kansa, wato ya zabi zama a wata kasa, saboda dalilai na yin kasuwanci, ko nazari , ko wasanni, ko aikin kimiya ko dai wani tsari da kasar ta tanada na baiwa jama’a iznin zama ’yan kasarta kamar yadda dokokin kasa da kasa suka tanada.

Wasu kasashen sun yarda da tsarin mallakar fasfo na kasa fiye da daya, wasu kuma hakan ya saba doka. Haka kuma ba wata kasa da za ta tilastawa wasu zama ’yan kasarta. Yin haka ya saba doka.

Wani mataki da kasar Burtaniya take shirin bullo da shi na zama “Hankaka mai da dan wani Naka” ya sa, daga ranar 31 ga watan Janairun shekarar 2021, kasar Sin ta sanar da cewa, ba za ta amince da fasfon da ’yan kasar Burtaniya da aka haifa a kasashen waje ba (BNO), a matsayin takardar da matafiya ke amfani da ita ko katin takardar shaidar zama dan kasa, kuma tana da ikon kara daukar matakin da ya dace kan wannan batu.

Ita dai kasar Sin ta dauki wannan mataki ne, bayan da gwamnatin Burtaniya ta sanar da cewa, za ta fara karbar takardun bukatun neman zama dan kasa da mazauna yankin Hong Kong na kasar Sin suka gabatar daga ranar 1 ga watan Fabrairun shekarar 2021

Burtaniya ta manta cewa, yankin Hong Kong ya dade da dawowa karkashin ikon kasar Sin, kuma yankin yana karkashin ikon kasar Sin ne, a don haka, bangaren Burtaniya ya keta alkawarin da ya yi, inda ya nace wajen samar da fasfo ga mazauna yankin Hong Kong, domin su zama ’yan kasar Burtaniya, har ma ta fafada tsarin gabatar da takardun neman bukatar fasfon.

Kafin yankin Hong Kong ya dawo karkashin ikon kasar Sin, Sin da Burtaniya sun cimma wata matsaya kan fasfon ’yan Burtaniya da aka haifa a kasashen waje (BNO), inda Birtaniya ta yi alkawarin cewa, mazauna yankin Hong Kong ba sa cikin wadanda za su amfana da wannan nau’i na fasfon, wanda dai za su samu damar zama a kasar Burtaniya..

Wannan mataki da Birtaniya ta bullo da shi a halin yanzu, tamkar shiga sharo ba shanu ne, kuma ya saba hadaddiyar Sanarwar da sassan biyu wato Sin da Birtaniya suka amince, a don haka, kasancewar yankin musamman na Hong Kong, wani bangare ne na kasar Sin, tana da izinin daukar martani idan bukatar hakan ta taso.

Sanin kowa ne cewa, irin wannan mataki, na neman mayar da al’ummar yankin Hong Kong tamkar rukuni na biyu na ’yan kasar Burtaniya, ya sauya tsarin ’yan asalin Burtaniya da aka haifa a ketare da aka cimma tsakanin bangarorin biyu. Haka kuma matakin ya keta ’yancin kasar Sin, kuma tsoma baki ne a harkokin yankin Hong Kong da ma na kasar Sin baki daya, sannan ya saba dokoki na kasa da kasa da muhimman ka’idojin hadin gwiwar kasa da kasa.

Duk wata kasa mai cikakken ’yanci ba kasar Sin kadai ba, dole ne ta yi Allah wadai matuka da ma adawa da wannan yunkuri na Burtaniya. (Ibrahim Yaya) 

Ibrahim