logo

HAUSA

Xinjiang Ta Samu Karuwar Cinikin Waje A Watan Mayu

2021-06-27 17:54:42 CRI

Xinjiang Ta Samu Karuwar Cinikin Waje A Watan Mayu_fororder_ciniki

Jihar Xinjiang ta Uygur mai cin gashin kai dake shiyyar arewa maso yammacin kasar Sin ta samu bunkasuwar harkokin kasuwanci na ketare da kashi 48.3 bisa 100 a watan Mayu, idan an kwatanta da makamancin lokacin bara, hukumar kwastom ta birnin Urumqi ta bayyana hakan.

A cewar hukumar, a watan Mayu, jimillar kasuwancin shigi da fici na jihar Xinjiang ta kai kudin Sin RMB yuan biliyan 12.54, kwatankwacin dalar Amurka biliyan 1.94. Adadin ya karu da kashi 21.9 bisa 100, idan an kwatanta da makamancin lokacin shekarar 2019.

Bugu da kari, sabbin alkaluman sun nuna cewa, hada-hadar kasuwancin waje na shiyyar ya karu da sama da kashi 30 bisa 100 a watanni uku a jere.

Hukumar ta bayyana cewa, bangaren injuna da kayan latironi, tufafin da kayayykin dinki, da takalma sun kasance a matsayin muhimman kayayyakin da aka fi fitarwa zuwa ketare daga shiyyar.(Ahmad)

Ahmad