logo

HAUSA

Jami’ar UNICEF ta bayyana damuwa game da hare hare kan kananan yara a yammaci da tsakiyar Afrika

2021-07-08 10:32:18 CRI

图片默认标题_fororder_src=http___images.news18.com_ibnlive_uploads_2018_10_Untitled-design21.png&refer=http___images.news18

Babbar daraktar asusun tallafawa kananan yara ta MDD (UNICEF), Henrietta Fore, ta bayyana damuwa game da karuwar hare haren da ake kaiwa kananan yara da kuma garkuwa da daliban makarantu a sassan yammaci da tsakiyar Afrika.

Cikin wata sanarwar da aka baiwa kwafenta ga kamfanin dillancin labarai na Xinhua, Fore ta ce, hukumar UNICEF ta nuna fargaba game da yiwuwar fuskantar karin hare haren kungiyoyin ‘yan bindiga a kasashen Burkina Faso, Kamaru, jamhuriya Afrika ta Tsakiya, jamhuriyar demokaradiyyar Kongo DRC, Nijer da Najeriya nan da wasu makonni masu zuwa.

Bangaren ‘yan sandan Najeriya ya ce, wasu gungun ‘yan bindiga da ba a san ko su wane ne ba sun kaddamar da hari kan makarantar Bethel Baptist dake garin Damishi a karamar hukumar Chikun dake jahar Kaduna a shiyyar arewa maso yammacin Najeriya, a ranar Litinin din da ta gabata, inda suka kwashe dalibai da ba a tantance adadinsu ba.

Fore ta kara da cewa, a baya bayan nan an hallaka fararen hula 178, ciki hadda kananan yara a Burkina Faso, sannan akwai sama da mutane miliyan 1.2 a Burkina Faso, amma kashi 61 bisa 100 na adadin sun kauracewa muhallansu sakamakon tashe tashen hankula, adadin da ya ninka sau 10 cikin shekaru uku da suka gabata.(Ahmad)

Ahmad