logo

HAUSA

UNICEF ya yi murna da sakin yara dalibai da aka yi garkuwa dasu a Najeriya

2021-02-28 15:27:33 CRI

Asusun tallafawa kananan yara na MDD (UNICEF) a jiya Asabar ya yi maraba da sakin daliban makarantar sakandaren kwana ta gwamnati wadanda aka yi garkuwa da su a arewa maso tsakiyar Najeriya.

Peter Hawkins, wakilin hukumar UNICEF a Najeriya, ya bayyana cikin wata sanarwa cewa, ya yi matukar farin cikin samun labarin sako yara daliban ’yan makarantar sakandaren kimiyya ta gwamnati dake garin Kagara su 27 bayan shafe sama da mako guda a hannun masu garkuwa da mutane don neman kudin fansa, kuma yana fatan za a sada su da iyalansu lami lafiya.

Jami’in ya ce, kaddamar da hare-hare kan makarantu mummunan keta haddin yara ne. Ya ce bai kamata a dinga kaddamar da hare-hare kan yara ba, a halin da ake ciki a Najeriya, ana yawan kaddamar da hare-hare kan yara, musamman a lokacin da suke makarantunsu.

A ranar 17 ga watan Fabrairu, wasu gungun ’yan bindiga suka tira a makarantar sakandaren kwana ta dalibai maza dake garin Kagara a karamar hukumar Rafi ta jahar Naija, inda suka yi garkuwa da mutane 42, 27 daga cikinsu dalibai ne, sai ma’aikatan makarantar 3 tare da iyalansu 12, yayin da suka kashe dalibi guda. (Ahmad)