logo

HAUSA

Somalia da UNICEF da ILO sun yi alkawarin kawo karshen bautar da yara

2021-06-13 16:12:23 CMG

Somalia da UNICEF da ILO sun yi alkawarin kawo karshen bautar da yara_fororder_0613-Somali-Ahmad

 

Kasar Somalia da asusun tallafawa ilmin yara na MDD, UNICEF, da kungiyar kwadago ta kasa da ILO, sun yi alkawarin daukar matakan kawo karshen bautar da kananan yara a kasar.

Yayin bikin zagayowar ranar yaki da ci da gumin yara ta kasa da kasa, bangarorin sun fidda sanarwar hadin gwiwa a Mogadishu, inda suka bayyana cewa, za a iya kawo karshen bautar da kananan yara ne kadai ta hanyar hadin gwiwa tsakanin bangarorin tare da kyakkyawar fahimtar matsalar tun daga tushe da kuma samar da cikakkiyar dokar haramta shigar da yara cikin ayyukan karfi yayin da suke kanana.

Gwamnatin kasar Somalia tana iyakar kokarinta wajen kawar da bautar da kananan yara a kasar. To sai dai kuma, har yanzu akwai sauran tafiya wajen tabbatar da cikakken sauyi game da halin da ake ciki.

Ministan kwadago da walwalar jama’a na kasar, Abdiwahab Ugas Khalif, yace, iyalai da dama suna tura ‘yayansu zuwa aikatau ne sakamakon matsin tattalin arziki da kuma rashin isassun ayyuka masu tsoka da magidanta ke fuskanta don wadata iyalansu.(Ahmad)

Ahmad