logo

HAUSA

UNICEF na neman kudi tallafawa yara miliyan 4.5 a kasar Sudan ta Kudu

2021-07-07 10:24:44 CRI

UNICEF na neman kudi tallafawa yara miliyan 4.5 a kasar Sudan ta Kudu_fororder_南苏丹

Asusun kula da yara na MDD UNICEF, ya ce yana fuskantar karancin kudin da ake bukata na taimakawa yara miliyan 4.5, yayin da ake fuskantar tabarbarewar yanayin jin kai a kasar Sudan ta Kudu.

Wani sabon rahoto da asusun ya fitar a Juba, gabanin cikar kasar shekaru 10 da samun ‘yancin kai, ya ce rikice-rikice da ambaliya da fari da sauran matsalolin yanayi da suka samo asali daga sauyin yanayi, sun yi tasiri kan fatan da ake da shi na kyautata rayuwar yara, baya ga ta’azzara matsalar tattalin arziki.

A cewar rahoton, wadannan yanayin sun kai ga tsananta matsalar karancin abinci, wanda ya zama daya daga cikin yanayin jin kai mai tsanani a duniya.

Babbar Daraktar asusun UNICEF, Henrietta Fore, ta ce rikice-rikice da cin zarafi ne suka mamaye rayuwar yara da dama ‘yan shekaru 10 a Sudan ta Kudu. Kawo yanzu, UNICEF ta karbi daya bisa ukun dala miliyan dala miliyan 180 da ta nema domin taimakawa yara mafi rauni a 2021. (Fa’iza Mustapha)