UNICEF: yara 33,000 na fuskantar barazanar mutuwa a yankin Tigray na Habasha
2021-06-15 10:37:38 CRI
Babban daraktan asusun yara na MDD UNICEF Henrietta Fore, ya yi gargadin cewa, akwai a kalla yara kanana 33,000 dake fuskantar barazanar mutuwa sakamakon yunwa dake addabar su, a yankin Tigray na kasar Habasha mai fama da tashe tashen hankula.
Mr. Fore, ya ce akwai yara kanana kimanin 56,000 ’yan kasa da shekaru 5 dake bukatar tallafin abinci sakamakon karancin abinci mai gina jiki, a gabar da jami’an agaji ke fuskantar kalubalen shiga yankin na Tigray, kuma rashin samun damar shigar da abinci yankin na iya hallaka yara kimanin yankin 33,000. (Saminu)