logo

HAUSA

Yin barci cikin dogon lokaci fiye da yadda ake bukata ko cikin gajeren lokaci sosai kan kara barazanar kamuwa da ciwon zuciya

2021-07-07 15:29:16 CRI

Yin barci cikin dogon lokaci fiye da yadda ake bukata ko cikin gajeren lokaci sosai kan kara barazanar kamuwa da ciwon zuciya_fororder_fs

Baya ga shan taba, shan giya da sauran batutuwan da suke kara barazanar kamuwa da ciwon zuciya, sanin kowa ne cewa, tsawon lokacin barci shi ma yana daya daga cikin muhimman batutuwan da suke illa ga lafiyar zukatan mutane. Wani nazarin da aka gudanar a kasa da kasa ya gano cewa, daukar dogon lokaci fiye da yadda ake bukata ko kuma gajeren lokaci sosai wajen yin barci, yana kara barazanar kamuwa da ciwon zuciya.

Wannan rahoton da aka wallafa shi a kwanan baya cikin mujallar hukumar ilmin ciwon zuciya ta kasar Amurka, wadda ake bugawa mako-mako, ya yi nuni da cewa, idan tsawon lokacin barci ya wuce sa’o’i 6 amma bai kai 9 ba a kowane dare, to, za a rage barazanar kamuwa da ciwon zuciya. Daukar dogon lokaci fiye da yadda ake bukata ko kuma gajeren lokaci sosai wajen yin barci, dukkansu suna kara barazanar.

Masu nazari daga babban asibitin Massachusetts na kasar Amurka da jami’ar Manchester ta kasar Birtaniya sun yi amfani da bayanan da suka shafi mutane fiye da dubu 461, wadanda aka ajiye cikin cibiyar adana samfuran kwayoyin halitta ta kasar Birtaniya. Masu nazarin sun tantance kwayoyin halittarsu, al’adarsu ta yin barci, bayanan ganin likita da dai sauransu, sun kuma dauki shekaru 7 suna gudanar da nazari kan wadannan mutane, wadanda shekarunsu suka wuce 40 amma ba su kai 69 da haihuwa ba, kana ba su yi fama da ciwon zuciya ba.

Masu nazarin sun yi la’akari da batutuwa guda 30, ciki hadda motsa jiki, arzikin da suka mallaka, lafiyar tunaninsu, yayin da suke gudanar da nazarin. Sun gano cewa, tsawon lokacin yin barci, wani batu ne dake tasiri kan barazanar kamuwa da ciwon zuciya. A wajen mutanen da suke fuskantar barazanar kamuwa da ciwon zuciya, idan suka dauki awoyi 6 zuwa 9 suna barci a kowane dare, to, zai rage barazanar da suke fuskanta da kaso 18 cikin 100. Wadanda tsawon lokacin barcinsu bai wuce awoyi 6 a kowane dare ba sun fi fuskantar karin barazanar kamuwa da ciwon har da kaso 20 cikin 100, in an kwatanta su da wadandan suke yin barci yadda ya kamata. Kana kuma, wadanda suke daukar awoyi fiye da 9 suna barci sun fi fuskantar karin barazanar har da kaso 34 cikin 100, in an kwatanta su da wadanda suke yin barci yadda ya kamata.

Masu nazarin ba su ci gaba da nazarinsu kan yadda tsawon lokacin yin barci ke karawa ko rage barazanar kamuwa da ciwon zuciya ba tukuna. Amma a baya wasu nazarce-nazarce sun taba yin karin bayani kan lamarin da cewa, yin barci cikin gajeren lokaci sosai kan yi illa ga lafiyar jijiyoyin zuciya da yadda kashi ke girma, tare da sanya mutane su ci ko su sha ta hanyar da ba ta dace ba. Idan an dauki dogon lokaci ana barci kuma, to, zai haddasa kumburi a jikin mutane, lamarin da ke da alaka da kamuwa da ciwon zuciya.  (Tasallah Yuan)

Tasallah Yuan