logo

HAUSA

Jinyar jarirai masu kamu da kwayoyin cutar AIDS da wuri zai kara amfanawa lafiyarsu

2021-06-21 10:25:16 CRI

Jinyar jarirai masu kamu da kwayoyin cutar AIDS da wuri zai kara amfanawa lafiyarsu_fororder_艾滋病02

Kwanan baya, masu nazari na kasar Amurka sun gano cewa, idan jarirai masu kamu da kwayoyin cutar AIDS sun fara samun jinya cikin awoyi ko kwanaki da dama bayan an haife su, to, za a kara kare tsarin garkuwar jikinsu.

Yanzu a kan yi wa jariran da suka kamu da kwayoyin cutar AIDS jinya cikin makonni ko watanni da dama bayan an haife su. A shekarar 2010, wata jaririyar da ta kamu da kwayoyin cutar AIDS a jihar Mississippi da ke Amurka ta fara samun jinya cikin awoyi 30 bayan an haife ta. Ko da yake bayan watanni 18, an dakatar da yi mata jinya, amma cikin watanni 27 baki daya ba a samu kwayoyin cutar ta AIDS a cikin jininta ba.

Jarirriyar ta sanya ma’aikatan lafiya gano iyuwar shawo kan cutar AIDS. Masu nazari daga jami’ar Harvard da kwalejin fasaha ta Massachusetts wato MIT a takaice, sun gudanar da nazari kan wannan fanni. Masu nazarin sun dauki shekaru 2 suna bibiyar jarirai 40 masu kamuwa da kwayoyin cutar AIDS na kasar Boswata, wadanda aka haife su a lokuta daban daban, amma an fara jinyar su cikin awoyi ko kwanaki da dama bayan an haife su.

Kwanan baya, masu nazarin sun tantance lafiyar wasu 10 daga cikin wadannan jariran Boswata da kuma lafiyar takwarorinsu 10 wadanda aka fara jinyar su bayan watanni 4 da aka haife su kamar yadda a kan yi. Masu nazarin sun kaddamar da rahoton nazarinsu a kwanan baya, inda suka bayyana cewa, idan an fara jinyar jarirai masu kamuwa da kwayoyin cutar AIDS cikin awoyi ko kwanaki da dama bayan an haife su, to, ba za a samu sassa da yawa da kwayoyin cutar za su yadu a jikinsu ba. Kana kuma wasu muhimman sassan tsarin garkuwar jikinsu suna cikin koshin lafiya.

Idan kwayoyin cutar ta AIDS sun kama mutane, to, kwayoyin cutar su kan taru a wasu sassan jikin mutane na gajeren lokaci. Wadannan sassan jikin dan Adam da aka fi samun kwayoyin cutar, suna fuskantar mummunan cikas wajen shawo kan cutar AIDS. Magungunan da aka ba wa masu kamuwa da cutar, suna iya hana karuwar yawan kwayoyin cutar a jikin mutane, amma ba su iya kashe kwayoyin cutar ba tukuna.

Masu nazarin sun yi nuni da cewa, sakamakon nazarinsu ya aza hasashe wajen shawo kan cutar ta AIDS baki daya daga tushe a nan gaba. (Tasallah Yuan)

Tasallah Yuan