logo

HAUSA

Wasu takardun bayanai sun fayyace shirin kasar Sin na aiwatar da sauye sauye a fanni kiwon lafiya a shekarar 2021

2021-06-18 11:29:31 cri

Wasu takardun bayanai da aka wallafa a shafin yanar gizo na majalissar gudanarwa ta kasar Sin a jiya alhamis, sun fayyace shirin gwamnati na aiwatar da sauye sauye a fanni kiwon lafiyar al’umma a shekarar nan ta 2021.

Takardun bayanan sun bayayana burin kasar Sin na samar da daidaito, tsakanin albarkatun kiwon lafiya da gina tsarin kiwon lafiyar kasar a bana.

Takardun sun kuma jaddada shirin mahukuntan Sin na gaggauta daidaita manufofi masu nasaba da hidimomin kiwon lafiya, da fannin inshora da sarrafa magunguna.

An bayyana cewa, Sin za ta rungumi tsarin sarin kayayyakin da ake bukata a fannin, da nufin zaftare farashin magunguna a wannan shekara ta 2021. Kaza lika an bayyana fatan cimma nasarar inganta tsarin binciken lafiya da jinya, da samar da ci gaba a fannin hidimomin kiwon lafiya.

Har ila yau, za a dora karin muhimmanci ga dakile yaduwar cututtuka cikin tsarin kiwon lafiyar kasar. Takardun bayanan sun kuma bayyana bukatar bunkasa matakan gargadi na gaggawa, da auna yanayin hadurra, da ayyukan gwajin cututtuka nan take.  (Saminu)