logo

HAUSA

Ta Yaya Kasar Sin Ta Yi Nasarar Kawar Da Cutar Malaria?

2021-06-30 20:48:18 CRI

Ta Yaya Kasar Sin Ta Yi Nasarar Kawar Da Cutar Malariya?_fororder_malariya

A yau ne hukumar lafiya ta duniya WHO, ta sanar da cewa, kasar Sin ta samu takardar shaidar hukumar dake tabbatar da cewa, ta yi nasarar kawar da cutar zazzabin cizon saura wato Malaria a kasar a hukumance. Wannan na nuna cewa, kasar Sin ita ce kasa ta farko a yammacin yankin fasifik, da ta samu irin wannan takardar shaida ta WHO a cikin sama da shekaru 30.

A shekarun 1940, adadin masu kamuwa da cutar zazzabin cizon sauro a kasar Sin, ya ragu zuwa mutane miliyan 30, sannan babu ko da mutum guda a shekarar 2017, har zuwa yanzu. Kasar Sin ta cimma wannan nasara ce, kan matakan kandagarki da hana yaduwar cutar da ta dauka. Haka kuma ta yi nasarar gina tsarin inshoran kiwon lafiya mai inganci. Wannan na daga cikin manyan nasarorin JKS na mayar da al’umma a gaban komai, kana a kullum tana dora muhimmanci kan rayuka da lafiyan jama’a.

A matsayinta na kasa mafi yawan al’umma a duniya, nasarar da kasar Sin ta cimma wajen kawar da cutar Malaria, ba kawai ya nuna yadda take kiyaye lafiyar al’umma ba, har ma ya shaida ci gaban da kasar ta samu a fannin kare hakkin bil-Adama. Wannan wata babbar gudummawa ce da kasar Sin ta bayar a fannin kiwon lafiyar bil-Adama da ma ci gaba a fannin kare hakkin bil-Adama a duniya, biyo bayan kawar da talauci.

Darekta mai kula da shirin WHO na yaki da zazzabin cizon sauro na Malaria a duniya Pedro Alonso, ya bayyana cewa, gwamman shekarun da gwmnatin kasar Sin da al’ummarta suka dauka suna gudanar da bincike da kirkire-kirkire, sun taimaka wajen hanzata ganin bayan cutar.  Wannan ya kara nuna kudirin kasar Sin na gina al’umma mai makomar bai daya a fannin kiwon lafiya,

Hakika, bil-Adama shi ne makomar bai daya. Magance matsalar lafiyar al’ummar duniya, goyon baya da hadin gwiwa, ita ce hanya mafi dacewa ga dukkan kasashe.(Ibrahim)

Ibrahim