logo

HAUSA

Kananan yara ‘yan kasa da shekaru 5 fiye da dubu 800 sun mutu a duniya a shekarar 2018 a sanadin ciwon huhu

2021-06-21 10:26:47 CRI

Kananan yara ‘yan kasa da shekaru 5 fiye da dubu 800 sun mutu a duniya a shekarar 2018 a sanadin ciwon huhu_fororder_f9198618367adab4de4f53356f91aa1a8601e4f1

Kwanan baya, asusun kula da kananan yara na MDD ya hada hannu da wasu kuniyoyin kasa da kasa wajen gabatar da wani rahoto, inda aka yi nuni da cewa, a shekarar 2018 da ta gabata, kananan yara fiye da dubu 800 a duniya wadanda shekarunsu ba su wuce 5 ba, sun rasa rayukansu sakamakon kamuwa da ciwon huhu, kwatankwancin yadda yaro ko yariya ‘yar kasa da sheakru 5 ke mutuwa sakamakon kamuwa da ciwon na huhu a ko wadanne dakikoki 39 a duniya.

Rahoton ya shaida cewa, ciwon huhu, mummunan ciwo ne da ke kashe kananan yara ‘yan kasa da shekaru 5 da haihuwa. Asusun kula da kananan yara na MDD da kawancen kula da harkokin alluran rigakafi na duniya da sauran kuniyoyin kasa da kasa, sun yi kira ga kasashen duniya da su dauki matakai wajen yaki da ciwon huhu dake halaka kananan yara.

Asusun kula da kananan yara na MDD ya yi bayani da cewa, a ko wace rana, kananan yara ‘yan kasa da shekaru 5 kusan dubu 2 da dari 2 ne suke mutuwa a sanadin ciwon huhu, wani nau’in ciwo da ake iya shawo kansa, kuma ana iya rigakafinsa a yawancin lokaci.

Dangane da lamarin, madam Zhang Chuji, wata likita ce da ke aiki a asibitin Tiantan na Beijing, ta yi mana karin bayani da cewa, hakika ana iya yin rigakafin ciwon huhu ne ta hanyar yin allura. Idan an tabbatar da kananan yara sun kamu da ciwon, to, za a iya jinyar su ta hanyar ba su magani mai sauki. Duk da haka ya zuwa yanzu, gomman miliyan kananan yara ne a duniya ba a yi musu alluran ba tukuna, haka kuma kananan yara da suka yi fama da ciwon huhu, wadanda yawansu ya kai kashi 1 cikin kashi 3 ba a yi musu jinya yadda ya kamata ba. Ko da yake kashi 15 bisa kashi 100 na kananan yara ‘yan kasa da shekaru 5 dake mutuwa a duniya, suna da nasaba da ciwon na huhu. Amma kudin da ake zubawa kan ciwon huhu ba shi da yawa, in an kwatanta kudin da ake kashewa kan sauran cututtuka. Kudin da aka kashe wajen yin nazari kan ciwon huhu ya kai kashi 3 cikin kashi 100 ne kawai bisa jimilar kudaden da aka kashe wajen yin nazarin cututtuka masu yaduwa a duniya.

Rahoton ya yi kira ga kasashen, da suka fi yaki da radadin ciwon huhu, da su tsara tare da aiwatar da manyan tsare-tsaren magance ciwon huhu, tare da kara bai wa al’ummarsu damar samun hidimar kiwon lafiya ta tilas. Haka zalika, rahoton ya kalubalanci kasashe masu wadata, da wadanda ke ba da taimako na kasa da kasa, da kamfanoni masu ruwa da tsaki, da su kara kudaden da aka kashe wajen samar da alluran rigakafin ciwon huhu, a kokarin kara yi wa kananan yara allura, da kuma kara zuba jari kan yin nazarin ciwon na huhu. (Tasallah Yuan)

Tasallah Yuan