logo

HAUSA

Xi zai halarci taron kolin shugabannin CPC da jam’iyyun siyasun duniya

2021-07-05 11:00:29 CRI

Mai magana da yawun sashen harkokin yin cudanya a tsakanin jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin da kasashen waje na kwamitin tsakiya na JKS Hu Zhaoming, ya sanar Litinin din cewa, babban sakataren kwamitin tsakiya na JKS Xi Jinping, zai halarci taron kolin shugabannin JKS da jam’iyyun siyasu na duniya da za a gudanar ta kafar bidiyo.

Xi Jinping zai halarci taron ne daga nan birnin Beijing, tare da gabatar da muhimmin jawabi.

Taken taron kolin shi ne” Inganta rayuwar jama’a: Nauyin dake wuyan jam’iyyun siyasu”. Hu ya bayyana cewa, sama da jagororin jam’iyyu da kungiyoyin siyasu 500 daga kasashe sama da 160 da sama da wakilan jam’iyyun siyasu 10,000 ne za su halarci taron kolin.

Ya kara da cewa, an shirya taron kolin ne a matsayin wani muhimmin taron diflomasiya na bangarori daban-daban, a dai-dai lokacin da JKS ta cika shekaru 100 cif da kafuwa.

Taron na da nufin, karfafa musaya da koyon dabaru a fannin shugabanci tsakanin JKS da sauran jam’iyyun siyasu a duniya baki daya, da hada kai don tunkarar kalubaloli na sauye-sauyen da ba a taba ganin irinsu ba a cikin wannan karni, gami da annobar COVID-19, da karfafa tsari na falsafa da dabarun samar da farin ciki ga al’umma, da ciyar da zaman lafiya da bunkasuwa a duniya, da bunkasa aikin gina al’umma mai kyakkyawar makoma ga daukacin bil-Adama. (Ibrahim)

Ibrahim