logo

HAUSA

Xi Jinping ya bukaci mambobin JKS da su taimakawa jama’ar kasar cimma burinsu

2021-07-01 10:35:52 CMG

A wajen bikin murnar cikar shekaru 100 ta kafuwar JKS, babban magatakardan jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin (JKS), Xi Jinping, ya yi kira ga daukacin mambobin jam’iyyar, da su tuna da burin da ‘yan jam’iyyar suka amincewa tun da farko, su aiwatar da babbar manufar jam’iyyar, da kare huldar dake tsakanin ‘yan JKS da jama’ar kasar Sin, ta yadda za su iya hadin gwiwa sosai, da kokarin neman cimma burin da jama’ar kasar suka sanya gaba, na kyautata zaman rayuwa, ta yadda za a kawo wa JKS, da jama’ar kasar Sin karin abubuwa na alfahari. (Bello Wang)

Bello