logo

HAUSA

Xi Jinping: Ba zai yiwu a raba kan JKS da jama’ar kasar Sin ba

2021-07-01 10:05:11 CMG

A yayin bikin murnar cikar shekaru 100 da kafuwar jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin wanda da ya gudana a yau Alhamis a birnin Beijing, babban sakataren jam’iyyar Xi Jinping, ya ce a ko da yaushe JKS tana wakiltar babbar moriyar daukacin jama’ar kasar Sin, kana ba ta da moriyar musamman ta kanta, wadda ba ta da wata alaka da moriyar wani gungun mutane, ko kuma wani jinsin musamman.

Ya ce duk wani mutum, dake son raba kawunan JKS da jama’ar kasar Sin, ba zai taba samun nasara ba. Xi Jinping ya jaddada cewa, dole ne JKS ta tsaya kan babbar manufarta ta kokarin bautawa jama’a, da neman samun ci gaba a ayyukan raya al’umma, da wadatar da daukacin jama’ar kasar. (Bello Wang)

Bello