logo

HAUSA

Xi Jinping ya jaddada bukatar gadon ruhin jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin na lokacin kafuwarta

2021-07-01 09:31:58 CMG

Babban sakataren jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin (JKS) Xi Jinping, ya jaddada a yau Alhamis cewa, cikin shekaru 100 da suka wuce, JKS ta yi kokarin gado, da yada ruhin da ta samu, a lokacin da aka kafa ta, tare da tabbatar da halayyar siyasa ta musamman ta ’yan jam’iyyar. Ya ce, ya kamata a ci gaba da gado, da kuma yayata ruhin har abada.

A cewarsa, yadda ake tsayawa kan gaskiya, da kokarin cimma burin da aka sanya tun da farko, da sauke nauyi, da biyayya ga JKS, da bautawa jama’a ba tare da tsoron sadaukar da kai ba, su ne ruhin JKS na lokacin kafuwarta, kana asali ne na karfin jam’iyyar. (Bello Wang)

Bello