logo

HAUSA

Shugabancin JKS Ne Ya Ingiza Ci Gaban Kasar Sin

2021-07-03 16:04:21 CRI

Shugabancin JKS Ne Ya Ingiza Ci Gaban Kasar Sin_fororder_sin

Zaunannen wakilin Sin a MDD Zhang Jun, ya ce riko da shugabancin JKS ne ya ingiza ci gaban kasar Sin.

Zhang Jun, ya bayyana wa zauren MDD a jiya, kwana 1 bayan kasar Sin ta yi bikin cika shekaru 100 da kafuwar JKS cewa, sirrin ci gaban kasar Sin shi ne riko da shugabancin jam’iyyar da lalubo hanyar samun ci gaba da ta dace da yanayin kasar, lamarin da ya ce ya samu goyon baya daga al’ummun kasar.

Zhang ya kara da cewa, a matsayinta na kasa mai tasowa mafi girma a duniya, kasar Sin tare da sauram kasashe masu matsakaicin kudin shiga, ta yi namijin kokarin raya tattalin arziki da zaman takewar al’ummar kasa.

Ya ce bisa irin kokarin dukkanin al’ummarta, Sin ta samu manyan nasarori a fannin ci gaba. Kana ta gina al’umma mai matsakaiciyar wadata ta kowacce fuska, tare da kawo mafita ga matsalar talauci a kasar.

Har ila yau, ya ce yanzu kasar na da kwarin gwiwa kan burinta na shekaru 100 na 2. Sin za ta ci gaba da zama mai ingiza zaman lafiya da ci gaban duniya, ba tare da la’akari da sauyin da duniya za ta fuskanta ba. (Fa’iza Mustapha)

Fa’iza Mustapha