logo

HAUSA

Shugaban kwamitin sulhun MDD ya ce za a gudanar da taruka gaba da gaba idan yanayin lafiya ya kyautata

2021-07-02 11:13:34 CMG

Shugaban kwamitin sulhun MDD ya ce za a gudanar da taruka gaba da gaba idan yanayin lafiya ya kyautata_fororder_ahmad-2

Nicolas de Riviere, jakadan kasar Faransa a MDD, kana shugaban taron kwamitin sulhun MDD na watan Yuli ya ce, za a gudanar da dukkan tarukan kwamitin sulhun MDDr gaba da gaba idan yanayin lafiya ya ba da damar yin hakan.

Ya ce a wannan watan na Yuli, dukkan tarukan kwamitin za su kasance fuska da fuska ne idan yanayin lafiya ya ba da damar yin hakan, de Riviere ya bayyanawa manema labarai a helkwatar MDD dake birnin New York.

Ya ce idan damar ta samu, babu yin taro ta kafar bidiyo. Don haka, dukkan mahalartan za su je wajen tarukan ne da kansu, wanda ya hada har da ministocin da aka gayyata.

Jakadan ya bayyana cewa, yin hakan abu ne mai muhimmanci kasancewar kwamitin sulhun MDD shi ma wani taron tattaunawa ne tsakanin wakilan kasashe 15. Kuma babbar manufarsa shi ne kokarin lalibo matsaya guda da nufin warware matsalolin rikice rikice.

Da yake jawabi game da ayyukan da aka tsara a wannan wata, de Riviere ya ce, akwai wasu muhimman ayyuka biyu da za a baiwa fifiko a wannan wata. Na farko ya shafi batun ayyukan jin kan bil adama ne. Na biyun kuma za a bayar da fifiko game da ayyukan majalisar na watan Yuli, kuma zai shafi batun yankin gabas ta tsakiya ne.(Ahmad)

Ahmad