logo

HAUSA

Wakilan Sin da Koriya ta Kudu sun nuna damuwa kan matakin Japan na zuba ruwan dagwalon nukiliya cikin teku

2021-06-24 11:19:26 CMG

Wakilan Sin da Koriya ta Kudu sun nuna damuwa kan matakin Japan na zuba ruwan dagwalon nukiliya cikin teku_fororder_fukushima

Jiya Laraba, yayin da ake gudanar da zama na 47 na majalisar kare hakkin dan Adam ta MDD, wakilan kasar Sin da na Koriya ta Kudu sun nuna damuwa game da shirin da kasar Japan za ta dauka na zuba ruwan dagwalon nukiliyarta na tashar lantarki ta Fukushima a cikin teku.

Jiang Duan, ministan kasar Sin a ofishin MDD dake Geneva, da sauran kungiyoyin kasa da kasa dake kasar Switzerland, ya ce wasu kwararru na majalisar kare hakkin dan Adam karkashin MDD sun riga sun bayyana damuwarsu dangane da lamarin. Inda kasar Sin a nata bangare ta yi kira ga kasar Japan da ta lura da damuwar da gamayyar kasa da kasa suka nuna, kuma ta soke matakinta na kuskure nan take. Kar ta zuba ruwa mai dauke da gubar nukiliya cikin teku, wanda zai iya lahanta lafiyar jama’ar kasashe makwabta da hakkinsu na ’yan Adam.

A nashi bangare, zaunanen wakilin kasar Koriya ta Kudu dake Geneva, mista Lee Tae Ho ya ce ya kamata gwamnatin kasar Japan ta bayyana kome a fili ba tare da wata rufa-rufa ba, kana ta yanke shawara bayan ta tattauna lamarin sosai tare da kasashe makwabta, da mai da aikin tabbatar da lafiyar jikin dan Adam, da kare muhallin duniya gaban kome. (Bello Wang)

Bello