logo

HAUSA

Sin da kasashe masu ra’ayi irin nata sun bayyana damuwa kan yadda ake yada labaran bogi game da ayyukan kare hakkin dan Adam

2021-07-03 15:56:58 CRI

Sin da kasashe masu ra’ayi irin nata sun bayyana damuwa kan yadda ake yada labaran bogi game da ayyukan kare hakkin dan Adam_fororder_1121195222_14981760785271n

Kasar Sin tare da wasu kasashe masu ra’ayi irin nata, sun bayyana damuwa game da yadda ake kitsawa da yada labaran bogi kan ayyukan kare hakkin dan Adam tsakanin kasa da kasa.

Babban jami’in tawagar kasar Sin a ofishin MDD dake Geneva, Jiang Duan ne ya bayyana haka, a madadin kasashen, yayin zama na 47 na hukumar kare hakkin dan Adam ta majalisar dake gudana.

Da yake gabatar da wata sanarwar hadin gwiwa, Jiang Duan ya ce wasu kasashe na kitsawa tare da yada labaran bogi saboda wasu muradu na siyasa, kana suna fakewa da batun kare hakkokin dan Adam wajen bata sunayen wasu, a yunkurinsu na samun damar tsoma baki cikin harkokin cikin gidan kasashe da yin gaban kansu wajen kakaba takunkumai masu tsanani da kuma daukar dabaru bisa ra’ayinsu a hukumar.

Ya kara da cewa, irin wadannan ayyuka sun take muradu da ka’idojin MDD. Haka kuma sun keta ka’idojin hukumar kare hakkin dan Adam, na kasancewarta ta kowa da kowa ba tare da nuna bangaranci ba. Yana mai cewa, babu abun da za su haifar face karkatar da ayyukan hukumar da kuma zubar da kimarsu.

Sanarwar hadin gwiwar ta bukaci kasashen da batun ya shafa su dakatar da shiryawa da yada labaran bogi, tare da kauracewa siyasantar da batun kare hakkin dan Adam. (Fa’iza Mustapha)

Fa’iza Mustapha