logo

HAUSA

Antonio Guterres ya bukaci a sassautawa kasashe masu matsakaicin kudin shiga a fannin biyan bashi

2021-06-18 12:59:36 cri

Babban magatakardar MDD Antonio Guterres, ya yi kira da a sassautawa kasashe masu matsakaicin karfin tattalin arziki, a fannin biyan bashin da ake bin su.

Mr. Guterres ya ce ana iya amfani da sabbin dabaru na sauya salon rage basussuka da ake bin irin wadannan kasashe, ta yadda za su kai ga iya fadada kasafin kudaden su, tare da bunkasa matakan farfadowa mai dorewa, bayan fuskantar kalubalen COVID-19.

Babban magatakardar MDDr yayi wannan tsokaci ne, yayin taron manyan jami’an majalissar da ya gudana a jiya Alhamis, inda aka tattauna game da yanayin da kasashe masu matsakaicin kudin shiga ke ciki.

Ya ce akwai bukatar samar da kudade ga wannan rukuni na kasashe, wadanda yawan su ya kai sama da rabin mambobin MDDr 193, ta yadda za su farfado daga matsin tattalin arziki da duniya baki daya ke fuskanta.

Mr. Guterres ya jaddada bukatar dagewa wannan rukuni na kasashe wa’adin biyan bashin su zuwa shekarar 2022 dake tafe, domin su samu zarafi farfado da yanayin zamantakewa da na tattalin arziki, wanda bullar cutar COVID-19 ya gurgunta.

Da dama daga kasashe masu matsakaicin karfin tattalin arziki dai na fuskantar matsi daga basussuka, tun ma kafin bullar annobar, wadda zuwan ta ya kara ta’azzara yanayin da suke ciki.  (Saminu)