logo

HAUSA

JKS Ta Cika Alkawarin Raya Zaman Al’umma Mai Matsakacin Karfi A Kasar Sin

2021-07-01 19:27:23 CRI

JKS Ta Cika Alkawarin Raya Zaman Al’umma Mai Matsakacin Karfi A Kasar Sin_fororder_jks

A yayin babban taron murnar cika shekaru 100 da kafuwar jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin da aka gudanar yau Alhamis 1 ga watan Yuli, Xi Jinping, babban sakataren kwamitin tsakiyar jam’iyyar ya sanar da cewa, kasar Sin ta tabbatar da manufarta ta raya zaman al’umma mai matsakaicin karfi daga dukkan fannoni a kasar, tare da kawar da kangin talauci, wanda ba a taba yi a baya ba. Kasar Sin tana nuna kuzari wajen cimma manufarta ta daban, wato tabbatar da raya kasar Sin ta zamani mai tsarin gurguzu nan da shekarar 2035, da kafa kasar Sin ta zamani mai tsarin gurguzu kuma mai karfi, wadata, bin tsarin demokuradiyya, wayin kai, jituwa da kyau nan da shekarar 2049 wato yayin da za a cika shekaru 100 da kafa jamhuriyar jama'ar kasar Sin.

Raya zaman al’umma mai matsakaicin karfi, alkawai ne da JKS ta yi wa jama’ar Sin a hukumance, haka kuma wani muhimmin mataki ne na tabbatar da farfado da al’ummar Sinawa baki daya. Yanzu JKS ta cika alkawarinta kamar yadda ta tsara, lamarin da ya nuna cewa, kasar Sin ta kai wani sabon mataki a fannonin tattalin arziki, kimiyya da fasaha, da zaman rayuwar jama’a da ma dukkan fannoni, haka kuma, ta samar wa kasashe da al’ummu a duniya wadanda suke fatan gaggauta raya kansu tare da samun ‘yancin kansu, hazakar Sinawa da dabarun kasar Sin, ta kuma ba da babbar gudummowa wajen ci gaban zaman al’ummar dan Adam.

Raya zaman al’umma mai matsakaicin wadata daga dukkan fannoni, wani aiki ne da JKS ta kammala a tarihi cikin nasara domin jama’a cikin shekaru 100 da suka wuce. Yanzu tana jagorantar jama’ar kasar Sin a kokarin tabbatar da manufarta dangane da kafa kasar Sin ta zamani mai karfi kuma mai tsarin gurguzu daga dukkan fannoni nan da shekarar 2049. Tabbatar da raya kasar Sin ta zamani, wata manufa ce da ‘yan jam’iyyar JKS take kokarin cimmawa ba tare da kasala ba. JKS za ta ci gaba da jagorantar jama’ar Sin a kokarin samun zaman rayuwa mai inganci, da kara bunkasa kasa, tare da sanya sabbin ci gaban da kasar Sin za ta samu, sun samar wa duniya sabuwar dama. (Tasallah Yuan)

Tasallah Yuan