logo

HAUSA

Xi Jinping: Daidaita batun Taiwan wani babban aiki ne na JKS

2021-07-01 10:20:15 CMG

A wajen bikin murnar cika shekaru 100 da kafuwar jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin (JKS), wanda ya gudana a yau da safe a birnin Beijing na kasar Sin, babban sakataren jam’iyyar Xi Jinping ya ce, wani babban aiki mai ma’ana a tarihi da JKS ke tsayawa a kai shi ne daidaita batun Taiwan, da dinkewar sassan kasar Sin waje guda. A cewarsa, bai kamata a raina cikakkiyar aniyar jama’ar kasar Sin, ta kare mulkin kai da cikakken yankin kasa, da kwazonsu a wannan fanni ba.

Ban da wannan, Xi Jinping ya ce ya kamata a aiwatar da manufofin “kasa daya mai tsarin mulki biyu”, da “barin mutanen Hong Kong da Macau su kula da harkokin wurarensu”, da ba su ikon cin gashin kai yadda ya kamata, da tabbatar da ikon sa ido na gwamnatin tsakiya kan yankunan musamman na Hong Kong da Macau, da tsarin shari’a na tabbatar da tsaron kasa a yankunan musamman, don cimma burin samun kwanciyar hankali da walwala, a yankunan Hong Kong da Macau na kasar Sin. (Bello Wang)

Bello