logo

HAUSA

Bai kamata kafofin watsa labarai na kasashen yamma su tsangwami ci gaban Xinjiang ba, in ji jakadan Somalia

2021-06-24 20:54:20 CRI

Bai kamata kafofin watsa labarai na kasashen yamma su tsangwami ci gaban Xinjiang ba, in ji jakadan Somalia_fororder___172.100.100.3_temp_9500049_1_9500049_1_6012_59c82718-1009-403d-a3b8-616a24749003

Jakadan kasar Somalia a kasar Sin Awale Ali Kullane, ya ce ko kadan, bai kamata kafofin watsa labarai na kasashen yammacin duniya, su tsangwami ci gaban jihar Xinjiang ta kasar Sin ba.

Jakada Kullane ya bayyana hakan ne, yayin wata zantawa da kafar CMG, inda ya ce, wasu kafofin watsa labarai na yammacin duniya sun rika kokarin sauya gaskiya, ta cikin rahotanni da suka rika watsawa, wanda hakan sam bai dace ba.

Ya ce yayin ziyarar da ya gudanar a baya bayan nan a jihar ta Xinjiang, ya ganewa idanunsa irin ci gaba ta fuskar tattalin arziki da zamantakewa da yankin ya samu, baya ga yadda ake kare da ma martaba al’adu mabambanta a yanki.

Jakadan ya ce "Yanzu haka Xinjiang na zaune lafiya, cikin daidaito da wadata. A gonaki, ko kamfanonin sarrafa auduga, da na saka tufafi, ana iya ganin al’ummun yankin cikin yanayin aiki mai kyau, kuma kwazon su ya sanya sun kaiwa ga fita daga kangin talauci, tare da samun wadata".

Mr. Kullane ya jaddada cewa, ko shakka ba bu, rahotannin suka da wasu kafofin yammacin duniya ke fitarwa game da Xinjiang, suna ruda masu sauraronsu. Kuma hakan rashin adalci ne ga kasar Sin. A hannu guda kuma, hakan na haifar da kalubale ga kasashen Afirka. Don haka ya zama wajibi a lalubo matakan warware wannan matsala, ta yadda al’ummun duniya za su rika samun rahotanni na gaskiya, daga sahihan kafofin watsa labarai.  (Saminu)