logo

HAUSA

Sin ta yi watsi da karairayin da Amurka take yayatawa game da jihar Xinjiang

2021-06-25 19:54:10 CRI

Sin ta yi watsi da karairayin da Amurka take yayatawa game da jihar Xinjiang_fororder_W020210625682300501627

A ‘yan kwanakin nan, Amurka ta sanya takunkumi kan wasu kamfanonin kasar Sin, bisa hujjar cewa wai ana tilastawa mutane yin aiki dole a jihar Xinjiang. Game da wannan batu, mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Zhao Lijian, ya bayyana cewa, Amurka ta sanya takunkumi kan kamfanonin Sin bisa hujjar da take cewa wai “hakikanin shaidu” ne, duk da cewa karairayi ne zalla da wasu Amurkawa suka kitsa, masu nasaba da jihar Xinjiang. To sai dai kuma kasar Sin ba za ta amince da hakan ba ko kadan.

Zhao ya jaddada cewa, yadda al’ummomi daban-daban a jihar Xinjing ke more rayuwarsu cikin zaman lafiya da kwanciyar hankali, gami da ci gaban hakkin dan Adam na kasar Sin baki daya, hakikanin gaskiya ce da bai dace a yi biris da ita ba. Don haka ya kamata Amurka ta mutunta gaskiya, ta dakatar da yayata labaran bogi da suka shafi kasar Sin, ta daina matsa lamba ga kamfanonin Sin babu gaira babu dalili. Domin kuwa kasar Sin za ta dauki duk wani matakin da ya wajaba, na kare halastaccen hakkin kamfanoninta.

Har wa yau, dangane da zargin da Amurka ta yi cewa wai kasar Sin tana cin zalin jaridar “Apple Daily” ta Hong Kong, Zhao Lijian ya ce, kamata ya yi Amurka ta girmama gaskiya, ta dakatar da duk wani yunkuri na kawo cikas ga ayyukan aiwatar da doka da oda a yankin Hong Kong na kasar Sin. Kaza lika ta dakatar da wanke wasu mutane daga munanan laifuffukan da suka aikata, tare kuma da daina yin shisshigi cikin harkokin gidan Hong Kong da na kasar Sin baki daya. (Murtala Zhang)