logo

HAUSA

Labarun Fararen Hula Jarumai Sun Bayyana Dalilan Da Suka Sa JKS Ta Yi Ta Samun Nasara

2021-06-29 21:17:49 CRI

Labarun Fararen Hula Jarumai Sun Bayyana Dalilan Da Suka Sa JKS Ta Yi Ta Samun Nasara_fororder_jks

A yayin bikin bayar da lambar karramawa ta “Ranar 1 ga Watan Yuli” da aka gudanar Talatar nan, babban sakataren kwamitin tsakiya na jam’iyyar Kwaminis ta kasasr Sin, wanda kuma shi ne shugaban kasar Sin, Xi Jinping ya gabatar da wani muhimmin jawabi, inda ya yi nuni da cewa, wadanda suka samu lambobin dukkansu fararen hula ne, suna kuma tsakanin jama’a, amma su jarumai ne da suka sadaukar da kansu ga ayyukansu.

Wanna shi ne karo na farko da aka bayar da lambar karramawa mafi daraja a tarihin JKS wato lambar “Ranar 1 ga Watan Yuli”. Wadanda suka samu lambobin su 29 ne, ko da yake ayyukansu da kuma shekarunsu na haihuwa sun sha bamban, amma dukkansu suna da kyawawan halaye na jajircewa da dagewa a matsayin ‘yan jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin. Sun sadaukar da kansu ga ayyukansu bisa tsayayyiyar aniya, suna da ladabi.

Idan an karanta labarun wadannan mutane 29, to, za a ga cewa, labarunsu, takaitaccen tarihi ne na yadda ‘yan jam’iyyar JKS suka yi gwagwarmaya domin jama’a. Kana kuma, ‘yan kasashen waje za su kara fahimtar JKS ta hanyar labarunsu.

A shekarar 1936, dan jaridar Amurka Edgar Snow ya tattara labaru a yankin da aka tafiyar da tsarin mulki iri na Soviet a arewacin lardin Shaanxi, ya kuma rubuta wani littafi mai suna Red Star Over China, littafin da ya taimakawa kasashen yammacin duniya kara fahimtar ‘yan jam’iyyar JKS, wato ‘yan jam’iyyar JKS da al’umma iyali daya ne, suna da kuzari, ‘yanci, mutunci da kyakkyawan buri, lamarin da ya sanya matasan kasar masu kishin kasa masu dimbin yawa da baki suka je Yan’an.

A cikin shekaru 100 da suka wuce, ‘yan jam’iyyar JKS suna jure wahala da samun ci gaba domin jama’a kuma bisa karfin jama’a, lamarin da ya sanya ‘yan jam’iyyar suka gaji kyakkyawan ruhu daga zuriya zuwa zuriya, kuma ba su canza burinsu na farko na shiga jam’iyyar ba. (Tasallah Yuan)

Tasallah Yuan