logo

HAUSA

Tsohon Shugaban Namibiya: Ci Gaban CPC Ya Amfanawa Kasar Sin Da Ma Duniya

2021-06-27 17:31:01 CRI

Manufar mayar da ci gaban rayuwar al’umma a gaban komai da jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin JKS ta tsara, ba kawai ta amfana wa al’ummun Sinawa kadai ba ne, har ma da al’ummun duniya baki daya, Sam Nujoma, shugaban kasar Namibia na farko shi ne ya bayyana hakan.

A wata hira da ya yi a kwanan nan da kafofin yada labaran kasar Sin, Nujoma ya taya babban sakataren kwamitin tsakiyar jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin Xi Jinping, da kwamitin tsakiyar JKS murnar cika shekaru 100 da kafuwar JKS, inda ya yaba wa muhimmin tarihin da ta kafa da manyan nasararon da kasar Sin ta cimma.

Wannan sanannen dan siyasar kasar Namibiya mai shekaru 92 a duniya ya ce, kasar Sin ta kasance a matsayin kasar da tattalin arzikinta yake saurin bunkasa a duniya, kuma JKS ce ta tsara dabarun da suka taimakawa kasar wajen samun muhimman nasarori a yaki da annobar COVID-19 da yaki da talauci, da kuma yadda tattalin arzikin kasar ke bukasa da kyautata zaman rayuwar al’ummar kasar.

Nujoma ya kara da cewa, da zummar tabbatar da bunkasuwar duniya da samar da makoma ga dukkan dukkan bil Adama, kasar Sin ta gabatar da tunanin gina al’umma mai kyakkyawar makoma ga dukkan bil Adama da kuma gabatar da sabbin manufofin kyautata mu’amalar kasa da kasa.

Ya ci gaba da cewa, Sin ta fadada manufofinta da kuma zurfafa manufar hadin gwiwar bangarori daban daban a sabon zamani, lamarin da ya samu matukar yabo da goyon bayan al’ummun kasa da kasa.(Ahmad)

Ahmad