logo

HAUSA

Tsarin dake iya kawo ci gaban kasa shi ne tsari mai kyau

2021-06-28 14:54:33 CMG

Tsarin dake iya kawo ci gaban kasa shi ne tsari mai kyau_fororder_JKS

Ranar 1 ga wata mai zuwa, ita ce ranar cikar jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin (JKS) shekaru 100 da kafuwa. Tun bayan kafuwar jamhuriyar jama’ar kasar Sin a shekarar 1949, jam’iyyar tana jagorantar ayyukan raya kasa da harkokin al’umma a kasar bisa matsayinta na jam’iyya mai mulki. Kana kundin tsarin mulkin kasar Sin ya kayyade cewa, jam’iyyar za ta ci gaba da rike ragamar mulki a kasar har abada. Sai dai wannan tsarin siyasa ya zama bai dace ba a idanun wasu mutane na kasashen yammacin duniya. A ganinsu, wannan tsari ya sabawa tunanin dimokuradiya.

Wani abun da ba su fahimta ba shi ne, akwai matsala a cikin tunaninsu game da tsarin dimokuradiya. Yadda kasashen yammacin duniya ke samun ci gaba da damar yin babakere a duniya, a fannonin tattalin arziki, da kimiyya da fasaha, da karfin soja, da siyasa, a cikin shekaru dari 2 zuwa dari 3 da suka gabata, ya sa kasashen ke dauke da ra’ayin cewar “Tsarin kasashen yammacin duniya tsari ne mafi kyau”. Amma a hakika, a nahiyoyin Afirka, da Latin Amurka, da Asiya ta tsakiya, kasashe da yawa sun gamu da matsala a lokacin da suke kokairn kwaikwayon tsarin dimokuradiya irin na yammacin duniya. Wasunsu sun tsunduma cikin yanayi na rikice-rikice, misali kasar Libya, da Afghanistan.

Sinawa sun san cewa tsarin siyasarsu shi ma wani tsari ne na dimokuradiya. Saboda a kasar Sin, ban da JKS dake kan karagar mulki, akwai sauran jam’iyyu 8, gami da mutanen da basa cikin wata jam’iyya, da suke ba da shawarwari kan harkokin siyasa. Suna taimakawa gwamnatin kasar wajen gabatar da manufofi masu kima, tare da sanya ido kan ayyukan jam’iyya mai mulki. Ban da wannan kuma, jama’ar kasar na zabar wakilansu ta hanyar jefa kuri’a, don kafa majalisar wakilan jama’a, wadda ke kula da ayyukan kafa doka, da sa ido kan aikin gwamnati. Wannan tsari, ko da yake ya sha bamban da na kasashen yammacin duniya, amma ya fi dacewa da yanayin da kasar Sin take ciki.

Idan mun yi la’akari da tarihi da al’adu na kasar Sin, za mu ga cewa, Sin ta zama wata dunkulalliyar kasa, inda gwamnatin tsakiya ke da cikakken ikon mulki, tun shekaru fiye da 2000 da suka wuce. Daga bisani, a karo da dama, Sinawa sun ganewa idonsu yadda kasar ke fama da rikice-rikice a lokacin da aka raba ta zuwa sassa daban daban, da yadda kasar ta sake zama mai karfi da tasiri yayin da ta samu tabbatar da dinkuwar sassanta waje guda. Sannu a hankali, Sinawa sun fara samun tunani na amincewa da dinkuwar kasa, gami da baiwa gwamnatin tsakiya cikakken ikon mulki.

Sa’an nan, idan mun dubi tasirin tsarin siyasa na kasar Sin, za mu gane cewa, tsarin nan na hadin gwiwar jam’iyyu daban daban karkashin jagorancin jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin (JKS) ya tabbatar da fannoni guda 2: Na farko, an tabbatar da samun kwanciyar hankali da hadin gwiwar al’umma. Inda a karkashin jagorancin JKS, dukkan jam’iyyu da kungiyoyin siyasa sun mai da cikakken hankali kan moriyar kasa da ta daukacin jama’ar kasar, maimakon moriyar wata jam’iyya ko kuma wani gungun mutane. Ta haka an samu magance rikicin jam’iyyu, da rarrabuwar kawuna a cikin al’umma. Sa’an nan, na biyu, an tabbatar da ingancin ayyukan tsarawa da gudanar da manufofi. Yadda jam’iyyu daban daban ke kokarin nuna goyon baya ga JKS, da taimaka mata wajen gudanar da mulki, ya sa ana iya tsara manufofi masu kima, da magance matsalar dadaddiyar tattaunawa ba tare da cimma matsaya ba, hakan ya sanya ake aiwatar da manufofin yadda ake bukata.

Wadannan fannoni 2 ne suka sanya ake samun kwanciyar hankali a kasar Sin, wata kasa mai kabilu 56, da yawan al’ummarta da ya kai fiye da biliyan 1.4. Kana sun taimaki kasar wajen samun ci gaban tattalin arziki cikin sauri, da tinkarar kalubaloli daban daban, irinsu bala’u, da annoba, da barazana a fannin tsaro.

Wani abu na daban da mutanen kasashen yammacin duniya suka kasa fahimta shi ne, ko da yaushe kasar Sin tana martaba tsarin siyasarta ta hanyar hakikanin ci gaban da kasar ta samu, amma sam ba ta nuna girman kai, kana ba ta son yayata tsarinta a duniya. Maimakon haka, gwamnatin kasar Sin ta sha jaddadawa a sau da dama cewa, kasar Sin tana girmama tsare-tsaren siyasar da sauran kasashe suka zaba, wadanda suka fi dacewa da yanayin da kasashen suke ciki. Dalilin da ya sa haka, shi ne domin Sinawa sun san cewa wani abu da ya fi kyau shi ne wanda ya dace da kai, kana tsarin dake iya kawo ci gaban kasa shi ne tsari mafi kyau. (Bello Wang)

Bello