logo

HAUSA

Manyan kusoshin kasashen waje sun taya murnar cika shekaru 100 da kafuwar JKS

2021-06-24 11:11:24 CMG

Manyan kusoshin kasashen waje sun taya murnar cika shekaru 100 da kafuwar JKS_fororder_jks

A ranar 1 ga watan Yuli mai zuwa, za a shirya bikin murnar cika shekaru 100 da kafuwar jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin (JKS). A wannan gaba, wasu manyan kusoshi na jam’iyyun siyasar kasashe fiye da 20, ciki har da na Falasdinu da Birkina Faso, sun mika sakon taya murna ga Xi Jinping, babban sakataren JKS, da kwamitin tsakiya na jam’iyyar.

Mahmoud Abbas shi ne shugaban alummar Falasdinu, da na jam’iyyar Fateh, wanda ya mika sahihiyar murna ga babban sakataren JKS Xi Jinping da jama’ar kasar Sin. A cewarsa, karkashin jagorancin Xi Jinping, kasar Sin ta samu babban ci gaba mai matukar burgewa a fannonin raya tattalin arziki, da kimiyya da fasaha, kana shawarar “Ziri Daya da Hanya Daya” da Mista Xi ya gabatar ta haifar da moriya ga bangarori daban daban.

A nasa bangare Blaise Compaoré, shugaban jam’iyyar neman ci gaban al’umma ta kasar Burkina Faso, ya ce ci gaban da kasar Sin ta samu abun mamaki ne, wanda ya sa ake girmama kasar sosai. Kana dalilin da ya sa kasar ke iya samun wannan ci gaba shi ne domin kasar ta zabi turbar tsarin gurguzu mai sigar musamman nata, da daukar takamaiman matakan raya tattalin arziki masu amfani, da ayyukan jagoranci masu kyau da JKS ta dade tana gudanar da su. (Bello Wang)

Bello