logo

HAUSA

Xi ya yi kira da a kara kaimi don cimma sabbin nasarori gabanin cikar JKS shekaru 100 da kafuwa

2021-06-28 20:00:41 CRI

Xi ya yi kira da a kara kaimi don cimma sabbin nasarori gabanin cikar JKS shekaru 100 da kafuwa_fororder_1127601143_16247091369331n

Yayin da ake shirin bikin cika shekaru 100 da kafuwar JKS, babban sakataren kwamitin tsakiya na JKS, kana shugaban kasar Xi Jinping, ya jaddada bukatar kara zage dantse, don cimma sabbin nasarori wadanda za su dace da zamani su kuma amfana wa jama’a.

Xi ya bayyana haka ne Jumma’ar da ta gabata, lokacin da yake yi wa wata tawagar nazari ta hukumar siyasar JKS jawabi.

Bayan kammala ziyarar wani gini mai hawa hudu da aka gina da jan bulu mai matukar muhimmanci a tarihin jam’iyyar, Xi ya yi kira da a kara fahimtar ka’idojin da suka kai ga ci gaban da aka samu a tarihin bil-Adama da kuma tsarin Markisanci.

Wannan gini a baya ya kasance tsangayar jami’ar Peking, inda wasu matasan Sinawa wadanda suka hada da Mao Zedong, sun gina ra’ayin Markisanci da ya kai ga kafa JKS. An kuma fara yada ra’ayin Markisanci a kasar Sin ne daga jami’ar.

Xi ya bayyana cewa, kafa zamantakewar al’ummar kwaminisanci, shi ne burin jam’iyyar kana manufar jami’yyar, a don haka, ya yi kira da a kara karfin zuciya kan tsarin gurguzu mai sigar musamman na kasar Sin.

Ya ce, aiwatar da ra’ayin Markisanci a zahiri, shi ne babban dalilin da ya sa JKS ta yi nasara, kana ana raya tsarin gurguzu mai sigar musamman na kasar Sin yadda ya kamata.(Ibrahim)

Ibrahim